Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London

Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London

- Pierre Emerick Aubameyeng ya rushe gidansa inda ya tamfatsa wani sabo a arewacin London

- Sabon gidan mai dakunan kwana bakwai yana alfahari da wasu irin kayan alatu na zamani

- Wurin adana motoci kadai wani tafkeken fili ne da aka yi shi a kasar gidan tare da wasu na'ura

Pierre Emerick Aubameyang ya zuba makuden kudi wurin gina sabon gida domin zamansa da iyalansa.

Gidan da ke arewacin birnin London, Aubameyang ya rushe tdohon gidansa ne inda ya gina sabon a filin.

Kamar yadda Sunsport ta wallafa, gidan me cike da kayan an yi shi ne ta yadda tauraron kungiyar kwallon kafa ta Arsenal din da bakinsa za su zauna hankali kwance.

Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London
Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London. Hoto daga priceypads.com
Asali: UGC

Daya daga cikin abubuwa masu matukar kayatarwa a cikin gidan ya hada da wurin motsa jiki da ke gidan kasa inda zai dinga motsa jiki.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama 'yan gidan fursuna da suka tsere da laifin fashi da makami

Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London
Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London. Hoto daga architecture.com
Asali: UGC

Katafaren gidan yana da sashin cin abinci inda zakaran dan wasan zai sakata ya wala.

A duk lokacin da aka kai wa dan wasan kwallon kafan ziyara, tunanin masaukin baki ba zai taba tada masa hankali ba tunda gidan na kunshe da dakunan bacci 7.

Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London
Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London. Hoto daga priceypads.com
Asali: UGC

KU KARANTA: FEC ta amince da fitar da N4.5bn domin titunan FCT da buga takardun jarabawa

Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London
Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London. Hoto daga priceypads.com
Asali: UGC

Akwai babban dakin shakatawa wanda aka yi shi daga saman bene.

Ko a hakan, garejin adana motocin shaharraren dan wasan babban abun kallo ne kuma ya dauki hankalin jama'a masu tarin yawa.

Fitaccen dan wasan kwallon kafan ya mallaki motocin alfarma wadanda za su kai darajar pam miliyan 3.

Daga ciki akwai wata irin mota kirar Ferrari LaFerrari wacce ta kai darajar pam miliyan biyu ita kadai, akwai Range Rover da Aston Martin.

Domin bai wa motocin alfarmar kariya, dan wasan kwallon kafan ya yi wurin adana su a gidan karkashin kasa wanda yake da na'urar dago su zuwa sama duk lokacin bukata.

Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London
Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London. Hoto daga priceypads.com
Asali: UGC

A wani labari na daban, 'Yan sandan jihar Kogi sun kama wani Fasto mai suna Sunday Edino da laifin satar kayan amfanin asibiti, wadanda za su kai kimanin Naira Biliyan 1.2.

An kama faston ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba, bayan kwamishinan 'yan sandan jihar, da yaransa sun bi gida-gida suna binciken kayan da matasa suka sata da sunan zanga-zangar EndSARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel