'Ina Fata,' Lionel Messi Ya Yi Magana kan Buga Gasar Kofin Duniya a 2026
- Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Argentina, Lionel Messi, ya bayyana cewa yana fatan taka leda a gasar cin kofin duniya ta 2026
- Lionel Messi ya ce zai duba lafiyarsa da yanayin jikinsa kafin ya yanke shawarar karshe kan shiga gasar a shekara mai zuwa
- Ya bayyana cewa buga gasar a karo na gaba na cikin abubuwan da yake fata a rayuwarsa bayan nasarar da suka samu a Qatar a 2022
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Argentina – Tauraron ƙwallon ƙafa na ƙasar Argentina, Lionel Messi, ya bayyana cewa yana da burin buga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 idan lafiyarsa ta ba shi dama.
Messi, wanda yanzu yake buga wasa a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, ya ce zai fara nazarin halin jikinsa a lokacin atisayen farko na kakar wasa mai zuwa kafin ya yanke hukunci.

Source: Getty Images
Ya bayyana hakan ne cikin wata hira da aka yi da shi a tashar NBC News a ranar Litinin, inda ya nuna cewa buga gasar a karo na gaba zai zama babban alfahari gare shi da ƙasarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kofin duniya: Messi zai duba lafiyarsa
Messi, mai shekaru 38, ya ce yana da sha’awa sosai ta kasancewa cikin jerin ‘yan wasan da za su wakilci Argentina a gasar kofin duniya ta 2026.
A cewarsa:
“Abu ne na musamman kasancewa cikin gasar cin kofin duniya, kuma zan so in kasance.
Ina fatan in kasance cikin koshin lafiya domin in taimaka wa ƙasata idan aka zaɓe ni.”
Messi, wanda zai cika shekara 39 a watan Yuni na shekara mai zuwa, ya ce zai yanke shawara bayan ya fara atisaye tare da Inter Miami don ganin ko jikinsa zai ba shi dama.
Messi na son buga gasar kofin duniya
Messi ya bayyana cewa sake buga gasar bayan nasarar da suka samu a Qatar a 2022 zai zama babban abin da ya ke fata.
Ya ce:
“Ina matuƙar son sake buga gasar, musamman bayan mun lashe ta 2022. Sake buga gasar zai zama abin alfahari saboda gasar duniya ita ce burin kowanne ɗan wasa.”
Messi ya fara buga wasa a matakin kwararru a shekarar 2004 tare da Barcelona, inda ya shahara sosai kafin ya koma Paris Saint-Germain a 2021, sannan daga bisani Inter Miami a 2023.

Source: Getty Images
Rahoton USA Today ya nuna cewa Messi ya ce yana jin daɗin rayuwa a birnin Miami inda yake tare da iyalinsa.
Messi, wanda shi ne ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a tarihin Argentina, ya buga wasanni 195 tare da cin ƙwallaye 114.
Obi ya yi magana kan wasanni a Najeriya
A wani labarin, mun rahoto muku cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya, Peter Obi ya yi magana kan harkar wasanni a Najeriya.
Peter Obi ya ce cin hanci da rashawa kan harkar wasanni sun kawo matsaloli da dama a kasar, musamman ga matasa.
Ya yi tsokaci game da wani filin wasa da ya ce hukumar FIFA ta bayar da kudi a gina a jihar Kebbi da ya ce kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


