An Fara Maganar Komawar Messi Saudiyya, Ya Buga da Ronaldo
- Lionel Messi na iya komawa kasar Saudiyya taka leda bayan bude tattaunawa tsakanin wakilansa da masu harkokin wasanni
- Dan wasan ya bayyana cewa tun da farko ya yi tunanin zuwa Saudiyya kafin ya yanke shawarar komawa Inter Miami a Amurka
- Zuwa yanzu ba a kammala wata yarjejeniya ba, amma yana iya komawa wata kungiya a Saudiyya daga watan Yuli, bayan karewar kwantiraginsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Gwarzon dan kwallon Argentina, Lionel Messi, na iya haduwa da tsohon abokin hamayyarsa, Cristiano Ronaldo, a kasar Saudiyya.
Messi da yanzu haka ke taka leda a kungiyar Inter Miami ta Amurka, na fuskantar karewar kwantiraginsa a karshen kakar 2025, sai dai akwai yiwuwar kara masa shekara daya.

Asali: Facebook
Shafin Goal da ke sharhi kan wasanni ya wallafa labarin bayan rahotanni sun tabbatar da bude tattaunawa tsakanin Messi da hukumomin Saudiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya daga Sport News ta bayyana cewa Saudi Public Investment Fund (PIF) ta sake bude tattaunawa da Messi domin jin matsayinsa kan yiwuwar komawa Saudiyya.
Messi ya taba tunanin zuwa Saudiyya
A cikin wata hira da ya yi a shekarar 2023, Messi ya ce ya yi la’akari da komawa Saudiyya kafin ya yanke shawarar zuwa Inter Miami.
Messi ya ce:
“Na dade ina tunani game da gasar Saudiyya. Na san kasar kuma suna kokari wajen gina gasa mai karfi wacce za ta zama abin kallo a nan gaba.
"Saudiyya ko MLS ne zabina, kuma kowanne daga ciki na burge ni sosai.”
Lionel Messi zai iya barin Inter Miami?
Ko da yake akwai batun kara masa kwantiragi da shekara guda a Inter Miami, har yanzu babu wata yarjejeniya da aka cimma.
Rahotanni sun ce Messi na iya barin kungiyar a matsayin dan wasa mai ‘yanci daga 1 ga watan Yuli, idan bai sabunta kwantiraginsa ba.
Wannan ne ya sa PIF ke kokarin fahimtar ra’ayinsa kan kaura zuwa Saudiyya domin taka leda idan wa'adin ya cika.
Messi zai iya haduwa da Ronaldo a Saudiyya
Idan Messi ya yarda da tayin komawa Saudiyya, zai iya haduwa da tsohon abokin hamayyarsa, Cristiano Ronaldo, wanda ke buga wa Al-Nassr wasa.
A halin yanzu ba a fayyace kungiyar da Messi zai koma ba, amma ana ganin Al-Hilal, Al-Nassr, Al-Ittihad da Al-Ahli na daga cikin kungiyoyin da zai iya komawa.
Hakan zai iya zama karo na farko da Messi da Ronaldo za su kara a gasar guda tun bayan barin Ronaldo Real Madrid a 2018.

Asali: Getty Images
Legit ta tattauna da masoyin Messi
Wani mai goyon bayan Messi, Muhammad Sa'idu ya ce zai so ganin dan wasan ya hadu da Ronaldo a Saudiyya.
Muhammad ya ce:
"Yana da kyau su kara haduwa a waje daya domin nuna wa Ronaldo har yanzu Messi yana gaba da shi.
Cristiano Ronaldo zai iya barin Saudiyya
A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen dan kwallo, Cristiano Ronaldo ya nuna alamun barin taka leda a kasar Saudiyya.
Legit ta fahimci haka ne bayan wani sako da Ronaldo ya wallafa a kafafen sada zumunta da yake nuna cewa zai sauya kasar taka leda.
Masu sharhi kan wasanni na ganin cewa Ronaldo zai dauki matakin ne domin cika burin da ya saka a gaba a harkokin kwallon kafa kafin ritaya.
Asali: Legit.ng