Tsohon Dan Wasan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Tsohon Dan Wasan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta sanar da mutuwar tsohon dan wasanta, Kevin Campbell bayan fama da jinya
  • Marigayin mai shekaru 54 ya rasu ne bayan fama da gajeruwar jinya a yau Asabar 15 ga watan Yuni a asibiti
  • Kungiyar Everton ita ma ta nuna alhini kan babban rashin tsohon dan wasan gabanta inda ta tura sakon ta'aziyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

London, England - Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Kevin Campbell ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin mai shekaru 54 wanda ya buga tamola a Everton ya rasu ne a yau Asabar 15 ga watan Yuni bayan fama da jinya.

Tsohon dan wasan Arsenal ya yi bankwana da duniya
Tsohon dan wasan Arsenal da Everton ya riga mu gidan gaskiya. Hoto: @Arsenal.
Asali: Twitter

Everton ta sanar da mutuwar Campbell

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya sun kwamushe mutum 18 bisa karya dokar aikin Hajji

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanar da kungiyar Everton ta fitar a shafinta na X a yau Asabar 15 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kowa a kungiyar Everton yana cikin alhini da kaduwa kan rashin tsohon dan wasan gaba, Kevin Campbell yana da shekaru 54."
"Ba iya jarumin Goodison Park ba ne kadai, Campbell ya kasance tauraro a kwallon Ingila gaba daya kuma mutum mai karimci."

- Kungiyar Everton

Arsenal ta nuna alhinin rasuwar Campbell

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ita ma ta nuna alhinin rashin Campbell a shafin X inda ta tura sakon jaje ga iyalan marigayin.

"Mun kadu da samun labarin rasuwar tsohon dan wasan gaba na Arsenal, Kevin Campbell bayan fama da rashin lafiya."
"Kowa yana son Campbell, dukkanmu muna jimami tare da abokansa da 'yan uwansa, ubangiji ya maka rahama, Kevin."

Kara karanta wannan

Ana tsaka da neman gurbi a kofin duniya, kocin Super Eagles, Finidi ya yi murabus

- Kungiyar Arsenal

Campbell ya buga wasa a kungiyoyin Arsenal da Everton da Nottingham Forest da sauran kungiyoyi a shekaru 20 da ya yi yana buga kwallo.

Ya zuwa kwallaye 148 a cikin wasanni 542 da ya buga kafin sauya layi zuwa bangaren aikin jarida inda ya samu shahara.

Finidi George ya yi murabus

Kun ji cewa kocin Super Eagles, Finidi George ya yi murabus daga jagorancin tawagar bayan rashin katabus a wasanni da ya yi.

Murabus din Finidi na zuwa ne yayin da Hukumar NFF ke kokarin dauko sabon koci daga kasashen ketare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.