Shahararren Dan Kwallon Najeriya Ya Lashe Kyautar Gwarzon Afirka Ta 2023, Ya Doke Salah, Hakimi

Shahararren Dan Kwallon Najeriya Ya Lashe Kyautar Gwarzon Afirka Ta 2023, Ya Doke Salah, Hakimi

  • Fitaccen dan kwallon kafa a Najeriya, Victor Osimhen ya lashe gwarzon dan wasan kwallon kafa a Nahiyar Afirka
  • Dan wasan ya kafa tarihi inda ya lashe kyautar wanda Nwankwo Kano ya lashe tun shekarar 1999
  • Osimhen ya kara da gwarazan ‘yan wasa kamar su dan kasar Masar, Mohammed Salah da Achraf Hakimi na kasar Morocco

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Marakesh, Morocco - Dan wasan kwallon kafar Najeriya, Victor Osimhen ya lashe kyautar zakarar dan kwallon kafa ta Nahiyar Afirka ta shekarar 2023.

Osimhen ya kara da gwarazan ‘yan wasa kamar su dan kasar Masar, Mohammed Salah da Achraf Hakimi na kasar Morocco.

Osimhen ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika ta 2023
Fitaccen Dan Wasan Najeriya, Osimhen Ya Lashe Kyautar Gwarzon Afirka Ta 2023. Hoto: CAF.
Asali: Facebook

Wane tarihi Osimhen ya kafa bayan lashe kyautar?

Kara karanta wannan

Kotu ta daure matashi wata 6 a gidan kaso saboda satar maggi da sabulu, Alkali ya ba shi zabi

An yi bikin ba da kyautar ce a birnin Marakesh da ke kasar Morocco da daren yau Litinin 11 ga watan Disamba, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Osimhen ya kafa tarihi inda ya sake lashe kyautar bayan shekaru 24 bayan Nwankwo Kano ya lashe kyautar a shekarar 1999.

Bayan lashe gasar, Osimhen cikin farin ciki ya godewa Emmanuel Amuneke da ya horas da shi a matakin 'yan wasan Najeriya kasa da shekaru 17.

Ya kuma godewa 'yan Najeriya bisa goyon baya da su ke ba shi da kuma magoya bayansa a fadin duniya.

Wani bajinta Osimhen ya yi a Napoli da ke Italiya?

Wannan nasara na da nasaba da irin bajintar da dan wasan ya nuna a kungiyar kwallon kafa ta Napoli da ke kasar Italiya, cewar CAF.

Dan wasan ya zura kwallaye 26 da hakan ya ba shi damar zaman dan Nahiyar Afirika da ya fi kowa zuwa kwallaye a shekarar.

Kara karanta wannan

Kotu ta ci tarar gwamnan Arewa miliyan 500 kan zargin take hakkin dan takara a zabe

Har ila yau, ya taimakawa Napoli ta ci gasar Serie A da kuma karya tarihin George Weah na dan Afirka da ya fi kowa kwallaye a Italiya.

'Yan wasan Afrika da su ka yi shura a Firimiya

A wani labarin, 'yan wasan kwallon kafa sa dama sun yi bajinta a gasar Firimiya ta Ingila.

Wannan rahoto ya kawo muku jerin 'yan wasan Nahiyar Afirka da su ka fi bajinta a gasar Firimiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel