Ronaldo Ya Fashe da Kuka Yayin da Al Nassr Ta Yi Rashin Nasara a Gasar Cin ‘Kofin Sarki’
- Cristiano Ronaldo ya zubar da hawaye bayan da kungiyarsa ta Al Nassr ta sha kashi a hannun Al Hilal a bugun fanariti a gasar cin kofin sarki
- Fitaccen dan wasan na Portugal, wanda ya zura kwallaye 58 a wasanni 64 a kungiyar Al-Nassr ya zube kasa a lokacin da Al Hilal ke murna
- Al-Hilal ta yi nasara da ci 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka tashi wasan farko da kunnen doki har zuwa karin lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jeddah, Saudiya - Cristiano Ronaldo ya zubar da hawaye bayan da kungiyarsa ta Al-Nassr ta sha kashi a hannun abokiyar hamayyarta Al-Hilal a ranar Juma'a da daddare a wasan karshe na cin 'kofin sarki'.
Tsohon dan wasan na Manchester United ya durkushe a kan guiwowinsa bayan da ‘yan wasa tara na Al-Hilal suka yi nasara da ci 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaron gida a Jeddah.
Al-Nassr ba ta daga kofi a bana ba
An lallashi dan wasan mai shekaru 39, wanda ya kafa sabon tarihin zura kwallo a gasar 'Saudi Pro League' da kwallaye 35, in da aka fitar da shi daga filin yana kuka, in ji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kyaftin din Portugal ya zura kwallaye 58 a wasanni 64 a kungiyar Al-Nassr tun bayan da ya koma kungiyar a watan Janairun 2023 bayan da ya bar United.
Kungiyar Al-Nassr ta tashi tutar babu a wannan kakar ba tare da wani kofi ba, amma a bara Ronaldo ya tsira da sarkar azurfa daya tilo a gasar cin kofin zakarun Larabawa.
Al-Nassr ta sha kashi hannun Al-Hilal
Channels TV ta ruwaito Al Nassr da Al-Hilal sun yi kunnen doki har bayan da aka kammala zagayen karin lokaci, lamarin da ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Bayan da tsohon dan wasan Wolves, Ruben Neves ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gidan Al-Hilal, shi ma tsohon dan wasan bayan United, Alex Telle ya kasa zura kwallon.
Kungiyoyin biyu sun ci bugun finareti hudu, ciki har da bugun Ronaldo, kafin mai tsaron gidan Al Hila, Yassine Bounou ya buge kwallon karshe da dan wasan Al-Nassr ya buga wanda ya ba Al-Hilal nasara.
Kalli bidiyon Ronaldo na kuka, wanda @UTDTrey ya wallafa a shafinsa na X.
Barcelona ta sallami kocinta Xavi Hernández
A wani labarin, mun ruwaito cewa FC Barcelona da Xavi Hernández Creus sun kawo karshen kwantiragin da ke tsakaninsu, inda kun giyar ta sallame shi da sauran tawagarsa.
Xavi, wanda ya buga wa Barça wasanni sama da 700 a matsayin dan wasa, ya karbi ragamar horar da kungiyar a shekarar 2021 kuma ya taimaka kungiyar ta daga kofi.
Asali: Legit.ng