Da duminsa: Ahmed Musa ya bar kungiyar Al Nassr da ke Saudi Arabia

Da duminsa: Ahmed Musa ya bar kungiyar Al Nassr da ke Saudi Arabia

- Fitacce kuma shahararren dan wasan kwallon kafa, Ahmed Musa ya bar kungiyar Al Nassr

- Kungiyar kwallon kafan da kanta ta yi wallafa hakan a shafinta na Twitter

- Ta yi wa shahararren dan wasan kwallon kafan fatan alheri a rayuwarsa da sauran wasanni a gaba

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na najeriya kuma kyaftin na kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Ahmed Musa, ya bar kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr da ke Saudi Arabia.

Musa ya bar kungiyar Al Nassr da ke kasar Saudi Arabia ne bayan kwashe shekaru 2 da yayi da kungiyar.

Da duminsa: Ahmed Musa ya bar kungiyar Al Nassr da ke Saudi Arabia
Da duminsa: Ahmed Musa ya bar kungiyar Al Nassr da ke Saudi Arabia. Hoto daga Getty Images
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Hotuna: Harkokin kasuwanci sun koma daidai bayan cire dokar kulle a Jos

Kungiyar Al Nassr ta sanar da hakan a wata wallafa da tayi a shafinta na Twitter a ranar Lahadi.

Kamar yadda ta bayyana, ta yi wa fitaccen dan wasan fatan alheri.

A wallafar, "Muna godiya kwararren dan wasan Najeriya Ahmed Musa, muna maka fatan alheri a nan gaba."

Dan wasan kwallon kafan mai shekaru 28 wanda ya bar kungiyar Leicester City a 2018, a halin yanzu bashi da kungiya.

A wani labari na daban, Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun karyata boye kayan abincin tallafin COVID-19 da kungiyoyi masu zaman kansu suka samar don sassautawa talakawa radadin zaman gida lokacin kullen COVID-19.

Kungiyar manyan 'yan kasuwa da kamfanoni wadanda suka taru suka kira kansu da CACOVID, sun hada biliyoyin nairori don taimakon 'yan Najeriya a kan cutar Coronavirus, wacce tayi ajalin mutane a kalla 1,139, sannan ta shafi mutane 62,992.

A cikin kudaden da suka hada an yi amfani da wasu don gina cibiyoyin kula da lafiya da magunguna cikin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Da duminsa: Dakarun sojin Najeriya sun fatattaki 'yan ta'addan da suka kai hari Borno

Yayin da aka yi amfani da wani bangare na kudin don siyan kayan abinci don rabawa talakawan da ke fama da yunwa yayin zaman gida.

Bayan an bayar da kayan abincin ne gwamnatin jihohi suka killace su a ma'adanar su, suna tunanin yadda za su raba kayan abincin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel