Rattaba Hannun Ronaldo a Al-Nassr Ya Jawowa Kulob Din Farin Jini, Ya Samu Sama da Mabiya 5.1m a Instagram

Rattaba Hannun Ronaldo a Al-Nassr Ya Jawowa Kulob Din Farin Jini, Ya Samu Sama da Mabiya 5.1m a Instagram

  • Sanuwar Christiano Ronaldo ya taimawa kulob din kasar Saudiyya, Al-Nassr wajen kara samun mabiya a Instagram
  • Kulob din na da kasa da mabiya miliyan daya kafin Ronaldo ya sanya hannu a kwanakin nan da suka gabata
  • Tsohon dan wasan na Real Madrid da Manchester United yana kokarin fara sabon aikin buga wasa a Al-Nassr

Al-Nassr, wata kulob din kwallon kafa a kasar Saudiyya ta fara ganin muhimmancin jawo Christiano Ronaldo cikinta ta hanyar habaka mabiya a kafafen sada zumunta.

Ronaldo dai bai fara buga kwallo ko daya ba a kulob din, amma mabiyansa sun yi ca tare da siyan riga mai suna da lambarsa don nuna goyon baya da kaunarsa.

Kafin Al-Nassr ta sanar da dauko Ronaldo, mabiyan kulob din a Instagram basu wuce 860k, amma cikin kwanaki biyu, sun karu zuwa sama da 6m.

Kara karanta wannan

Shekarar 2022 Ta Zama Shekarar Zulumi Da Fargaba, Akalla Mutum 8,000 Ne Suka Rasa Ransu a Shekarar

Al-Nassr ta daukaka bayan zuwan Ronaldo
Rattaba Hannun Ronaldo a Al-Nassr Ya Jawowa Kulob Din Farin Jini, Ya Samu Sama da Mabiya 5.1m a Instagram | Hoto: dailymail.co.uk
Asali: UGC

Ronaldo da kansa dai na da mabiya mafi yawa a Instagram kuma wannan na nufin mabiyansa sun fara bibiyar Al-Nassr a yanzu kasancewar zakinsu ya koma can.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Ronaldo ya rabu da Manchester United, ya buga wasan cin kofin duniya

Idan za ku iya tunawa, Ronaldo na da matsaloli da manyan masu tafiyar da kulob din Manchester United kafin daga bisani aka dakatar da aikinsa a kulob din.

A watan Disamba ne ya yi tafiya zuwa kasar Qatar don bugawa kasar Portugal wasan cin kofin duniya.

An cire kasarsu ta Portugal a wasa na biyun kusa da karshe a jerangiyar wasannin da kasashen duniya suka buga gasar ta cin kofin duniya.

Ronaldo dai na ci gaba da daukar hankali a duniyar kwallon kafa tun shekarar da ta gabata, wannan ya fara ne tun bayan da ya bar kulob din Real Madrid, inda tauraruwarsa ta haska.

Kara karanta wannan

Ku Tashi Tsaye, Ku Nemi Makami Ku Kare Kanku, Shahararren Gwamnan Arewa Ya Fada Wa Mutanen Jiharsa

Ronaldo zai tashi da €400m a shekaru 2, ya shiga kulob din Saudiyya

A bangare guda, bayan shafe dan lokaci a kasa, dan wasan Manchester United, Ronaldo ya samu sabuwar kulob din da zai fara bugawa wasa.

Al-Nassr, wata kungiyar kwallon kafa ce a kasar Saudiyya, kuma ta dauko Ronaldo don buga mata wasanni a nan gaba.

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, akalla Ronaldo zai tashi da zunzurutun kudi €400m cikin shekaru biyu kacal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel