Ibrahim Magu
Za ku ji cewa wani ya kai karar Shugaban hukumar zabe na kasa gaban Kotu a Najeriya. Hon. Emmanuel Agonsi shi ne ya shigar da wannan kara mai lamba a Abuja.
EFCC ta koma gaban Alkali da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal. Ana zargin Injiniya Babachir David Lawal da satar Naira miliyan 544.
Wani shaidan da EFCC ta kira a kotu ya tona badakalar da aka yi a baya inda Kamfanoni da ‘Yan Majalisa su ka rika raba ribar da aka samu kwangilolin mazabu.
A 2020, Alkalai sun daure mutane 800 a cikin kara 1300 da EFCC ta kai Kotu. Hukumar EFCC ta gurfanar da mutane 1300 a gaban kotu a shekarar nan da za ta fita.
Za a saurari daukaka karar da Olisah Metuh da kuma Kanal Sambo Dasuki su kayi. A gobe ne hukumar EFCC, Dasuki da Metuh duk za su san abin da zai faru da su.
Hukumar EFCC ta rasa karar da ta shigar da tsohon Minista, Ambasada Aminu Wali a kan satar kudin kamfe a zaben 2019. Kotu ta wanke tsohon Ministan a makon jiya.
Mun tattaro maku wasu ‘Yan siyasa da su kayi uzuri da ciwo bayan sun ji babu haza gaban Alkali. Uwar bari ta sa marasa gaskiya suna zuwa kotu da keken guragu.
Mista Abdulrasheed Abdullahi Maina ya sulale zuwa Nijar bayan an bada belinsa a kotu. Mutumin da ake nema ruwa a jallo, ya batar da kama, ya yi fasfon bogi.
A jiya mu ke jin cewa EFCC ta bukaci a daga shari’a zuwa 2021 bayan ta gaza kamo Diezani Alison-Madueke. Tun 2015 Alison-Madueke ta bar Najeriya, har yau shiru.
Ibrahim Magu
Samu kari