Kotun daukaka kara za ta yanke hukunci a kan shari’ar Metuh da Dasuki
- Za a saurari daukaka karar da Olisah Metuh da kuma Sambo Dasuki su kayi
- A ranar Laraba ne babban kotun daukaka kara za ta zauna ta yanke hukunci
- Ana zargin Dasuki da Metuh da laifin cin amana da cin kudin da bai halatta ba
Babban kotun daukaka kara da ke Abuja ya sa gobe Laraba, 16 ga watan Disamba, 2020, a matsayin ranar da zai saurari shari’ar Olisa Metuh.
Jaridar Punch ta ce an sanar da lauyoyin tsohon mai magana da yawun bakin jam’iyyar PDP cewa za a zauna domin sauraron kara uku da aka daukaka.
Alkali mai shari’a Stephen Adah da wasu mutum uku ne za su zartar da hukunci a gobe da rana.
Lauyan Olisa Metuh da wanda ya tsayawa kamfanin Destra Investment Limited su ne su ka daukaka shari'a zuwa kotun daukaka kara na kasa.
KU KARANTA: Ban yi wa Buhari aiki a lokacin da na ke tare da Jonathan ba - Dasuki
A shari’ar da aka yi a kotun tarayya, an ba tsohon sakataren yada labaran PDP, Olisa Metuh da kamfaninsa watau Destra Investment rashin gaskiya.
Jaridar ta Punch ta ce kara ta uku da aka daukaka ita ce wanda tsohon mai bada shawara a kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dauki mai ritaya ya shigar.
An samu Sambo Dasuki da laifin cin amana da kuma aikawa Olisa Metuh da kamfaninsa kudin haram.
A farkon shekarar nan ne Alkali Okoh Abang ya samu Metuh da laifi, ya kuma yanke masu hukuncin daurin shekara bakwai a gidan gyaran hali.
KU KARANTA: A ware Dasuki daga shari'ar kudin makamai - EFCC
Dasuki ta lauyansa, Joseph Daudu ya na kalubalantar hukuncin da aka yi, yace zartar masa da hukuncin da aka yi ba tare da yana nan ba, ya saba doka.
A jiya kun ji cewa sauya-shekar Yakubu Dogara ta sa jam'iyyar PDP ta hada da shi da APC, INEC, Majalisar wakilai da AGF duk ta maka a gaban Kotun Abuja.
Jam’iyyar PDP ta shiga kotu da tsohon ‘Dan majalisarta saboda yayi ridda, ya koma APC. PDP ta ce babu dalilin da zai sa Dogara ya tsere bayan ya lashe zabe.
Lauyan PDP ya ce dole Dogara ya fice ya bar majalisa, kuma ya dawo da kudin da aka biya shi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng