Tinubu Zai Rage Jami'an Hukumomi da Ke Yawan Bincike a Filayen Jiragen Sama

Tinubu Zai Rage Jami'an Hukumomi da Ke Yawan Bincike a Filayen Jiragen Sama

  • Yayin da fasinjoji ke korafe-korafe kan yawan bincike a filayen jiragen sama, gwamnati za ta dauki mataki
  • Hukumar FAAN da ofishin Nuhu Ribadu sun yi haɗaka domin rage jami'an hukumomi da ke yawan bincike a filayen jiragen sama
  • Wannan na zuwa ne yayin da fasinjoji ke yawan korafi kan bincikensu da ake daga jami'ai daban-daban a kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya za ta rage yawan jami'an tsaro da ke binciken kayayyaki a filayen jiragen sama.

Hukumar kula da jiragen sama ta FAAN da ofishin mai ba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro domin tabbatar da haka.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dawo da lantarki a garuruwan da aka yi shekaru babu wuta a Sokoto

Tinubu zai rage jami'an hukumomi da ke bincike a filayen jiragen sama
Bola Tinubu ya tabbatar da shirin rage jami'an hukumomi da ke yawan bincike a filayen jiragen sama. Hoto: Festus Keyamo, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Wane mataki FAAN ta ɗauka?

Hukumar ta ce za ta rage yawan jami'an ne daga hukumomi daban-daban a filayen jiragen saman, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

FAAN ta ce ta dauki matakin ne domin saukaka tafiye-tafiye yayin da fasinjoji ke kokawa kan yawan binciken a filayen jiragen saman Najeriya.

Babbar manajan hukumar, Olubunmi Kuku ita ta bayyana haka a jiya Asabar 4 ga watan Mayu a Legas.

Kuku ta ce sun yi haɗaka da ofishin NSA domin rage yawan binciken da ake yi a filayen jiragen sama, cewar BusinessDay.

Za a saka CCTV a filin jirgin sama

Babbar manajan ta ce za su yi haɗaka wurin amfani da na'urar CCTV a ofis domin tabbatar da ingancin aikinsu.

Har ila yau, Kuku ta ce sun yi magana da Nuhu Ribadu domin ganin an dakile matsalar da ta addabi matafiya.

Kara karanta wannan

Karshen 'yan bindiga ya zo, gwamna ya shirya sanya hannu a wata doka, ya yi gargadi

"Abin ya wuce batun FAAN, akwai hukumomi da dama a filayen jiragen sama da suke yin bincike kan matafiya wanda ya yi yawa."
"Akwai hukumomi kamar NDLEA da Kwastam da kuma EFCC da sauransu da ke cike a filayen jiragen sama domin bincike daban-daban."

- Olubunmi Kuku

Kuku ta ce suna kokarin rage yawan jami'an hukumomi da ke bincike domin inganta yadda za a ci gaba da duba fasinjoji da kayayyakinsu.

"Ba zamu zargi Buhari ba", Kashim

Kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana tsare-tsaren da Shugaba Bola Tinubu ya kawo.

Shettima ya ce yanzu ba lokacin zargin gwamnatin Muhammadu Buhari ba ne illa hanyar neman mafita ga matsalolin ƙasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel