Babu hannun Amb. Aminu Wali a zargin wawurar kudin yakin neman zabe inji Kotu

Babu hannun Amb. Aminu Wali a zargin wawurar kudin yakin neman zabe inji Kotu

- An kawo karshen shari’ar da ake yi tsakanin Hukumar EFCC da su Aminu Wali

- Alkali ya wanke Aminu Wali, yace babu abin da ke gaskata zargin da ake yi masa

- Lauyan EFCC yace zasu duba hukuncin shari’ar da ta ba Tsohon Ministan nasara

Babban kotun tarayya da ke Kano ta wanke tsohon Ministan harkokin waje, Amb. Aminu Wali, daga zargin da hukumar EFCC ta ke yi masa.

Ana zargin Ambasada Aminu Wali ne da laifin sace Naira miliyan 950 da aka tanada domin yakin neman yakin zaben jam’iyyar PDP tun a 2019.

Jaridar Daily Trust tace Alkali ya wanke tsohon Ministan da wani tsohon kwamishinan ayyukan gwamnatin jihar Kano, Mista Mansur Ahmed.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta shigar da karar Aminu Wali da Mansur Ahmed a gaban kuliya.

KU KARANTA: Kankara: Atiku ya ba Shugaba Buhari shawara

EFCC tana tuhumar wadannan mutane biyu da karbar kudi ta hanyar da ta saba dokar safarar kudi ta 2011.

Alkali mai shari’a, Lewis Allagoa, yace EFCC ba ta iya gamsar da kotu cewa wadanda ake tuhuma, sun aikata laifin da ake jifarsu da aikata wa ba.

A dalilin gaza war Lauyoyin gwamnati ne Lewis Allagoa ya wanke wanda ake zargi, ya sake su.

Lauyan da ya tsaya wa wanda ake zargi da laifi, Sam Olagunorisa, ya bayyana cewa ya yi farin ciki da hukuncin da wannan Alkalin kotun ya dauka.

KU KARANTA: NDDC ta samu sabon Shugaba

Babu hannun Amb. Aminu Wali a zargin wawurar kudin yakin neman zabe inji Kotu
Aminu Wali Hoto: GettyImages
Source: Getty Images

Sam Olagunorisa ya ce: “Mun iya gamsar da kotu cewa kudin sun bi ta hanyoyin da suka hallata.”

Shi kuwa Lauyan EFCC, Cosmos Ogwu, cewa ya yi: “Mun zo karshen wannan tafiya, za mu duba hukuncin da aka yi, mu ga matakin da za mu dauka.”

Kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci iyalan mutum 16 'yan garin Danbatta da suka rasu a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Bayan ya aika ta'aziyya, Gwamnan ya bawa kowane iyalan wadanda suka mutu kyautar naira 100,000.

Kamar yadda mu ka samu rahoto, Gwamnan ya tunatar da iyalan mamatan cewa abinda ya faru kaddara ne daga Allah, ya kuma shawarce su da rike addu'a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel