Hukumar EFCC: Ba a yi min adalci ba, in ji Ibrahim Magu

Hukumar EFCC: Ba a yi min adalci ba, in ji Ibrahim Magu

- Tosin Ojaomo, lauyan dakataccen shugaban hukumar EFCC ya yi martani kan nadin sabon shugaban EFCC da Shugaba ya yi

- Ojaomo wanda aka yi hira da shi a ranar Talata ya ce ba a yi wa Ibrahim Magu adalci ba domin ba a sanar da sakamakon bincike ba

- Ya kara da cewa baya ga Magu akwai wasu a hukumar ta EFCC da aka dakatar kuma har suma ba a sanar da sakamakon binciken ba

- Ojaomo ya ce rashin bayyana wa al'umma sakamakon binciken na iya taba mutunci da kimar wadanda aka bincika

Lauyan tsohon shugaban riko na hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta'annati, EFCC, Tosin Ojaomo a ranar Talata ya koka kan cewa ba a yi adalci ba a game da batun Ibrahim Magu.

Ojaomo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' da The Nation ta bibiya.

Hukumar EFCC: Ba a yi min adalci ba, in ji Ibrahim Magu
Hukumar EFCC: Ba a yi min adalci ba, in ji Ibrahim Magu. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Umar Faruk: Matashin da aka yanke wa hukunci saboda ɓatanci a Kano ya bar Nigeria

An kaddamar da kwamitin Ayo-Salami ne domin yin bincike game da dakataccen shugaban rikon kwaryan na hukumar yaki da rashawar.

Ya ce: "kwatsam, rahoto bai fito ba, sai aka yi wani nadin ... ana iya gani karara cewa ba a yi wa Magu adalci ba a wannan batun, muna magana kan mutuncin da kimar mutane ne a nan.

"Ba Magu kadai abin ya shafa ba, akwai wasu mutane a hukumar da aka dakatar da su, dukkan mutanen nan, suna iya rasa kimarsu kamar an manta da batunsu ne.

"Idan ana batun adalci, na kan tuna da kalaman Mai shari'a Oputa, wanda ya yi magana kan adalci, ya ce akwai abubuwa 3 a batun adalci: adalci ga wanda ya yi kara, adalci ga wanda ake zargi da adalci ga al'umma.

KU KARANTA: Hotunan ganawar Buhari, Zulum, Buni da dattawan Borno da Yobe a Aso Rock

"A wannan batun, ba a yi wa yan Nigeria adalci ba domin kowa na sa ran sanin sakamakon binciken. Akwai labarai da yawa game da Magu a kafafen watsa labarai, yanzu an bar mutane cikin waswasi."

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164