Zargin sata: Kotu na bukatar ganin Alison-Madueke a ranar 3 ga watan Maris

Zargin sata: Kotu na bukatar ganin Alison-Madueke a ranar 3 ga watan Maris

-Hukumar EFCC ba ta iya kawo Diezani Alison-Madueke gaban kotu ba

-Lauyan EFCC ya roki Alkali ta kara masu lokaci kafin su iya fito da ita

-Ana zargin tsohuwar Ministan man Najeriyar da laifin satar kudin kasa

A ranar Alhamis, 4 ga watan Disamba, 2020, Alkalin babban kotun tarayya dake garin Abuja ta ba EFCC karin lokaci domin ta fito da Diezani Alison-Madueke.

Jaridar Punch ta ce Mai shari’a Ijeoma Ojukwu, ya ba hukumar EFCC zuwa ranar 3 ga watan Maris, 2021 ta kawo tsohuwar Ministar man Najeriya gabansa.

A zaman jiya, Lauyan dake kare EFCC, Barista Farouk Abdullah, ya roki a kara masa lokaci kafin hukumar ta iya kamo wanda ake zargi, Misis Alison-Madueke.

KU KARANTA: AGF: Kotu ta bukaci ganin hujjar kama Alison-Madueke

Farouk Abdullah ya ke sanar da kotu cewa: “Masu tuhuma sun dauki matakai na ganin cewa an bi umarnin kotu. Ba mu kai ga nasara ba, amma mun yi yunkuri.”

EFCC ta yi dace, Alkalin ta dage wannan shari’a zuwa ranar 3 ga watan Maris, 2021 domin karbar rahoto game da shirin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Bayan nan ne kuma ake sa ran cewa za a fara shari’a tsakanin wannan Baiwar Allah da gwamnati.

“A dalilin haka, ina rokon a daga wannan lamari domin masu tuhuma su yi abin da kotu ta ce.”

KU KARANTA: Diezani Alison Madukwe ta samu mukami a kasar Dominican Republic

Zargin sata: Kotu na bukatar ganin Alison-Madueke a ranar 3 ga watan Maris
Tun 2015 Alison-Madueke ta bar Najeriya Hoto: Twitter/AlisonDiezaniMadueke
Source: Twitter

A watan Yulin 2020, Alkali ta aika takarda ta na neman Diezani Alison-Madueke a gaban kotu.

Misis Diezani Alison-Madueke wanda ta rike kujerar Ministar man fetur a gwamnatin PDP, tuni ta tsere zuwa kasar waje, don haka ta ki bayyana a gaban kotu.

A dalilin haka ne a watan Oktoba, EFCC ta roki Kotu a bada umarnin a cafko ta duk inda aka kama ta.

Alkali mai shari’a Ijeoma Ojukwu ba ta amince da bukatar EFCC ba, a karshe ta bukaci hukumar ta kinkimo tsohuwar Ministar zuwa gida domin ayi mata shari’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel