An Shiga Jimamin Rashin Daliba Aishat a Jami’ar Aliko Dangote Bayan Tsintar Gawarta a Daki

An Shiga Jimamin Rashin Daliba Aishat a Jami’ar Aliko Dangote Bayan Tsintar Gawarta a Daki

  • Jami’ar Aliko Dangote ta fitar da jawabi kan gaskiyar abin da ya faru a mutuwar wata daliba ‘yar aji uku
  • Dalibai sun bayyana yadda dalibar ta rasu a cikin dakinta da ke wajen makaranta bayan rubuta jarrabawa
  • Ba sabon lamari bane samun mutuwar dalibai a ciki ko wajen jami’a ba, hakan ya sha aukuwa a wurare da dama

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kano - Wani mummunan lamari ya afku a ranar Alhamis a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Jihar Kano, inda aka tsinci gawar wata daliba mai suna Aishat Yahaya Olabisi a wani gidan da take zaune a wajen jami’ar.

Kara karanta wannan

Kano: An tsinci gawar dalibar jami'ar Aliko Dangote a dakin kwananta

An tsinci gawar Aishat, wacce daliba ce ‘yar aji uku a fannin fasahar abinci da kimiyya bayan ta dawo dakinta daga makaranta.

An tsince gawar daliba a jami'ar Kano
An tsince gawar daliba a dakinta a Kano | Hoto: Aliko Dangote University of Science and Technology
Asali: Facebook

An kuma ce, dalibar da ta rasu ta rubuta jarrabawarta ta farko a zangon farko na shekarar karatu ta jami’ar, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane yanayi Aishat take kafin shigarta jarrabawa?

Daya daga cikin daliban da ta zanta da jaridar Punch a ranar Asabar ta dora laifin rasuwar ta fuji’a da matsin jarrabawa.

A cewarta:

“Lafiyarta kalau lafin ta tafi rubuta jarrabawarta ta farko a zangon farko da ake gudanarwa.”

Sai dai, bayan jita-jitar da aka yada cewa dalibar ta rasu ne a dakin karatun da ke cikin jami’ar, tuni mahukunta a jami’ar suka fayyace komai.

Bayanin da jami’ar Aliko Dangote ta fitar

A wata sanarwar da shugaban kula da harkokin dalibai na jami’ar, farfesa Abdulkadir Dambazau ya fitar a ranar 3 ga watan Mayu, ya ce ba a cikin jami’ar ta rasu ba.

Kara karanta wannan

Fatima Alkali: Ɗalibar da ta rikita Arewa bayan ta yi kacal kaca da jarabawar UTME

Ya kuma bayyana matakan da jami’ar ta dauka na binciken inda dalibar take bayan rashin ganinta, inda daga baya aka gano ta mutu a dakinta.

Ya zuwa yanzu, an dauki gawar Aishat zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke birnin Kano don bincika gawar.

An tsince gawar daliba a UNIPORT

A wani labarin kuma, kun ji yadda aka tsince gawar wata dalibar jami’a a jihar Rivers a cikin dakinta.

Wannan lamari ya tada hankali, inda tuni aka fara binciken sanadiyyar mutuwarta tare da daukar mataki.

A cewar majiya, dalibar ta mutu a dakinta da ke wajen makaranta bayan ta dawo daga karatu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel