Maina: Mutumin da ake nema ido-rufe, ya bad-da-kama, ya yi fasfon bogi, ya tsere

Maina: Mutumin da ake nema ido-rufe, ya bad-da-kama, ya yi fasfon bogi, ya tsere

- Abdulrasheed Abdullahi Maina ya sulale zuwa Nijar bayan an bada belinsa a kotu

- Bincike ya nuna Mista Abdulrasheed Maina ya batar da kama ne, ya tsere kan babur

- Maina yayi wasu takardun karya, ya canza waya domin Jami’ai su gagara gano shi

Bayanai sun bayyana a game da yadda aka kama Abdulrasheed Abdullahi Maina, a kasar makwabta, mutumin da ake ta nema a Najeriya.

Vanguard ta ce Abdulrasheed Abdullahi Maina, tsohon shugaban kwamitin da aka kafa domin gyarar harkar fansho ya sulale ne zuwa kasar Nijar.

Jami’an ‘yan sanda a karkashin jagorancin CP Garba Baba Umar ne su ka kutsa har babban birnin Niamey a kasar Nijar, su ka cafke wannan mutumi.

KU KARANTA: Ina asibiti a Najeriya, ba ni da lafiya - Maina

An yi ram da Malam Abdulrasheed Abdullahi Maina ne a ofishin jakadancin kasar Amurka da ke Niamey, inda ya yi karyar shi mutumin Amurka ne.

Abdulrasheed Maina ya yi takardun bogi ne da su ka ba shi damar labewa a Jamhuriyyar Nijar.

Bayan haka, rahoto ya nuna cewa tsohon jami’in gwamnatin ya rika amfani da waya kirar Thuraya ne domin jami’an tsaro su gagara gane inda ya labe.

Duk da wannan dabaru, ‘yan sandan Najeriya ba su gagara gano Malam Maina ba, su ka cafke shi, kuma su ka dawo da shi domin cigaba da shari’arsa a kotu.

KU KARANTA: Amurka ta sa Najeriya cikin kasashe masu tsangwamar addini

Maina: Mutumin da ake nema ido-rufe, ya bad-da-kama, ya yi fasfon bogi, ya tsere
Abdulrasheed Maina Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Abdulrasheed Maina ya boye a Nijar ne bayan Alkali ya sa a karbe takardunsa, sai da ya ajiye fasfon Najeriyarsa da na Amurka kafin ya iya samun beli.

Maina ya yi amfani da babur ne, ya faki idanun jami’an da ke kan iyakokin Najeriya a jihar Sokoto, ya tsere zuwa Nijar, a karshe ya sake shiga hannun hukuma.

Bayan abin nan ya faru, kun ji cewa Sanata Ali Ndume wanda ya tsaya wa Maina, ya umarci lauyoyinsa su fara shirye-shiryen zame shi daga shari'arsa.

Sanatan na jihar Borno, Ali Ndume ya yi kwanaki biyar a garkame a kurkuku a sakamakon tsaya wa Maina da yayi, shi kuwa ya tsere ya bar shi a tashin hankali.

A halin yanzu Alkali ya bukaci a adana Abdulrasheed Maina a gidan yari har sai an gama shari'a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng