Lanbo ko ciwo: Jerin manyan da su ka zama marasa lafiyan dole a zauren shari’a

Lanbo ko ciwo: Jerin manyan da su ka zama marasa lafiyan dole a zauren shari’a

Ana yawan zargin ‘yan siyasa da masu mulki a Najeriya da rashin gaskiya wadanda su ka hada da sata, almundahana da baba-kere da dukiyar al’umma.

Yayin da ake bincike ko shari’a, ya zama salo na wadannan manya, sai su marairaice da sunan su ba su da lafiya. Babu tabbacin cewa su na da wata larura.

Mun kawo jerin fitattun manyan da su ka fadi a kotu ko a zauren majalisa ko su ka zo a mirgine:

1. Olisa Metuh

Olisa Metuh ya rike kujerar Mai magana da yawun bakin PDP, da ake shari’a da shi bisa zargin karbar kudi a hannun Sambo Dasuki, sai ya buge da rashin lafiya, har da zuwa kotu a motar gawa.

KU KARANTA: Maina ya fadi a kotu

2. Bello Halliru Mohammed

Tsohon shugaban PDP, Alhaji Bello Haliru Mohammed ya taba zuwa gaban Alkalin babban kotun tarayya a kotu a kan kujerar guragu domin ya tabbatar da cewa ya na fama da rashin lafiya.

3. Dino Melaye

Sanata Dino Melaye ya na cikin shaharrun ‘yan siyasa a Najeriya. Shi ma ya taba zuwa kotu rage-rage a motar daukar gawa bayan ‘yan sanda sun kama shi bisa zargin mallakar makamai.

4. Kemebradikumo Pondei

KU KARANTA: An cafke Faisal Maina

Lanbo ko ciwo: Jerin manyan da su ka zama marasa lafiyan dole a zauren shari’a
Masu ikirarin ciwo a kotu Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Da ‘yan majalisa su ke binciken Kemebradikumo Pondei da laifin tafka badakala a hukumar NDDC, sai kwatsam ya marairace, ya rika fiki-fiki da idanu, Allan-barin cewa bai da lafiya.

5. Abdulrasheed Maina

Na karshe a jerin na mu shi ne Abdulrasheed Maina, wanda shi ne sabon shiga wannan dabara. A yau Alhamis ne Maina ya kife a kotu, bayan an yi nasarar kamo shi domin cigaba da shari’a.

Dazu kun ji cewa kotu ta sa a tsare Farfesan jami'ar Uyo a Najeriya, Ignatius Uku a kurkuku a kan zarginsa da ake yi da hannu wajen tafka magudin zabe a Akwa Ibom.

Bayan yi masa barazanar daure shi, Farfesa Uduk ya bayyana gaban Alkali a ranar Laraba. Wannan malami zai shafe kwana 5 a gidan maza kafin ya samu beli.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel