Gwamna Ya Shirya Daukar Mataki Mai Tsauri Kan Dan Kwangila Saboda Aikin N6bn

Gwamna Ya Shirya Daukar Mataki Mai Tsauri Kan Dan Kwangila Saboda Aikin N6bn

  • Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya ja kunnen ɗan kwangilar da aka ba aikin gina titin garin Bori
  • Gwamnan ya umurci ya koka kan yadda duk da ya biya ɗan kwangilar kuɗaɗe masu yawa kan aikin, amma yana tafiyar hawainiya
  • A cewar gwamnan na jam'iyyar PDP ko dai ɗan kwangilar ya koma bakin aiki ko kuma ya kunya ta shi a idon duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya gargaɗi ɗan kwangilar da ke kula da aikin hanyar cikin garin Bori da ya kammala shi nan ba da daɗewa ba ko kuma ya fuskanci hukunci mai tsauri.

Gwamnan ya ce duk da an cika kaso 80% na sharuɗɗan kwangilar, ɗan kwangilar yana yi wa aikin tafiyar hawainiya.

Kara karanta wannan

Sanatan NNPP ya hango kuskure a kasafin kudin 2024 da Tinubu ya sa hannu

Fubara ya gargadi dan kwangila
Gwamna Fubara ya gargadi dan kwangila ya dawo bakin aiki Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Gwamna Fubara ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci wurin da ake gudanar da aikin a garin Bori, hedkwatar ƙaramar hukumar Khana ta jihar Ribas a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me gwamnan ya ce kan aikin?

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Nelson Chukwudi ya fitar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Wannan aikin an bayar da shi ne kafin in shiga ofis. Amma na biya kuɗi sau biyu domin wannan aikin. Adadin kuɗin wannan aikin ya haura N6bn."
"A watan Yunin shekarar 2023, na biya N2bn na farko, kuma a watan Disamban 2023, na sake fitar da N2bn, wanda ya kai kusan kaso 80% na kuɗin aikin."
"Domin haka, na yi mamakin yadda wani zai ce ba mu son kammala wannan aikin wanda yake a mazaɓata ta Sanata."

Kara karanta wannan

An samu barkewar wata cuta a Adamawa, mutum 42 sun rasa ransu

"Ba na so na ambaci sunan ɗan kwangilar, domin kada a ce saboda wani abu ne. Amma ɗan kwangilan ya san kansa."
"Ya kamata ya koma wurin aiki ko kuma na yi wani abu da zai ba shi kunya a matsayinsa na mutum."

Kwamishinoni sun yi murabus a Ribas

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamishinoni huɗu a majalisar zartarwar jihar Ribas sun ajiye aikin da gwamna Siminalayi Fubara ya naɗa su.

Kwamishinonin da suka ajiye aikin sun haɗa da kwamishinan ayyuka George Kelly, kwamishinan wutar lantarki Henry Ogiri, kwamishinan shari'a Farfesa Zacchaeus Adango da kwamishinan kudi Isaac Kamalu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel