"Jama'a Sun Ƙosa a Yanzu": Sarkin Musulmi Ya Kuma Jan Hankalin Shugabanni

"Jama'a Sun Ƙosa a Yanzu": Sarkin Musulmi Ya Kuma Jan Hankalin Shugabanni

  • Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya ba shugabanni shawara kan neman hanyar kawo karshen matsalolin Najeriya
  • Sultan ya shawarci 'yan ƙasar da su dage wurin tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu ba tare da nuna bambanci ba
  • Mai Martaba ya ce a yanzu 'yan Najeriya sun matsu domin ganin sun samu sauyi a kasar ganin halin da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - Mai Martaba, Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya kalubalanci shugabanni kan samar da shugabanci nagari.

Sultan ya ce 'yan Najeriya sun zaƙu domin ganin sauyi a kasar cikin gaggawa saboda halin da ake ciki.

Sarkin Musulmi ya kalubalanci shugabanni kan jagoranci nagari
Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya bukaci shugabanni su kawo karshen matsalolin Najeriya. Hoto: @sultan_ofsokoto.
Asali: Twitter

Sarkin Musulmi ya bukaci sauyi a Najeriya

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Sarkin Musulmi ya fadi abin da talakawa za suyi wa shugabanni

Mai Martaba ya bayyana haka a jiya Asabar 4 ga watan Mayu yayin bikin cika shekaru biyar kan karagar mulki na Sarkin Lafia, Sidi Bage-Mohammed.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci 'yan Najeriya da su ba zaman lafiya da hadin kai fifiko domin samun damar fita daga ƙangin da ake ciki, cewar Daily Trust.

Har ila yau, ya shawarci 'yan ƙasar da su dage da addu'a musamman ga shugabanni domin samun damar shugabantarsu yadda ya kamata.

Sai dai ya kalubalanci shugabanni da su samar da duk wata hanya da za ta dakile matsin tattalin arziki da rashin tsaro da ake fama da su, cewar ThisDay.

Sarkin Musulmi ya kalubalanci shugabanni

"Mun sani shugabanni suna iya bakin kokarinsu amma ya kamata su dage domin kawo sauyi a Najeriya."
"Yan Najeriya sun matsu suga an samu sauyi ganin halin da ake ciki yanzu musamman rashin tsaro da matsin tattalin arziki."

Kara karanta wannan

An shiga fargaba bayan 'yan bindiga sun shiga garuruwan Katsina, an hallaka mutane 24

"Ku duba yadda sarakunan gargajiya suka cika wannan taro daga dukkan bangarorin kasar, wannan ya na nuna akwai hadin kai a tsakani, ina rokon sauran 'yan kasa su yi koyi da haka."

- Sa'ad Abubakar

Sultan ya gargadi shugabanni a Najeriya

A wani labarin mai kama da wannan, Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya bukaci shugabanni su yi dukkan mai yiwuwa domin dakile matsalolin kasar nan.

Sultan ya ce a yanzu sun kure matasa ba za su iya shawo kansu ba idan har aka ci gaba da tafiya a irin wannan hali.

Ya bukaci a dakile matsalar tsaro da kuma samar da ayyuka ga matasa wanda shi ne babban matsalar da ke damunsu a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel