Siyasar Najeriya
A jiya Abdulaziz Yari ya bayyana a ofishin EFCC a Legas, ya sha tambayoyi. Jami’an EFCC sun rutsa Jigon APC, Yari, ya yi sa’o’i kafin a sallame shi da yamma.
Ghali Na’Abba, Utomi, Sonaiya, Moghalu da Agbakoba za su kafa Jam’iyya da za ta karbi mulki. Za a kafa wannan jam’iyya ne a watan gobe na Maris a za a shiga.
Fasto Tunde Bakare ya bayyana cewa Gwamnatin Muhammadu Buhari ta gaza. Tsohon abokin tafiyar na Buhari ya ce kowa na cewa shugaba Buhari ya ba mutane kunya.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya zugo Matasa cewa tsofaffin kwanonin nan ba za su mika maku mulki ba, ya ce sai dai su tashi su fizgi kujerun mulki.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Kabiru Gaya ya bayyana cewa ya kamata a bari yankin kudancin kasar ta samar da shugaban kasa a 2023 idan har ana son adalci.
Tsohon ‘Dan takarar Shugaban kasa ya fadi yankin da zai sha wuya idan Najeriya ta barke. Ya ce ba Arewa ba, sauran bangarori ne za su sha wahala idan ake rabu.
Mun samu labari cewa yaran Biodun Olujimi sun daukaka kara bayan an ba bangaren Fayose nasara a rikicin Ekiti. Sun ce za su kai bangaren Ayo Fayose kotun koli.
Kungiyar Afenifere da kuma PDP sun soki Gwamnonin jihohin da su ka yi bataliya zuwa Daura. Su ka ce abin kunya ne Gwamnoni har 10 su yi zuga, su tafi Daura.
Wasu ‘Yan APC sun bangare, sun fito da APC Pressure Group a Jihar Katsina. Wannan sabon rikicin cikin gida ya shiga APC a Katsina har ya sa ‘Yan taware sun ware
Siyasar Najeriya
Samu kari