2023: Ƙungiyar arewa ta bayyana sanata daga kudu da ta ke son ya gaji Buhari

2023: Ƙungiyar arewa ta bayyana sanata daga kudu da ta ke son ya gaji Buhari

  • Kungiyar 'Grassroots Mobilisers Association of Northern Nigeria', (GMANN) ta ce babu wanda ya dace ya gaji Buhari a 2023 kamar Orji Kalu
  • Kungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin shugabanta na kasa Alhaji Murtala Mohammed a ranar Litinin inda ya lissafa dalilan su na goyon bayan Kalu
  • Alhaji Murtala ya ce Kalu yana da kwarewa sosai a bangarori da yawa na rayuwa kasancewarsa dan kasuwa na duniya, tsohon gwamna kuma yanzu sanata

Gabanin babban zaben 2023, kungiyar arewa ta 'Grassroots Mobilisers Association of Northern Nigeria', (GMANN) ta nuna goyon bayan ta ga dan kudu maso gabashin Najeriya ya zama shugaban kasa na gaba, Guardian ta ruwaito.

Ta kuma nuna cewa tana son tsohon gwamnan jihar Abia kuma babban bulaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022

2023: Ƙungiyar arewa ta bayyana sanata daga kudu da ta ke son ya gaji Buhari
Kungiyar arewa ta nuna goyon bayanta ga Orji Kalu ya gaji Buhari a 2023. Hoto: Guardian
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Murtala Mohammed ya ce:

"Samun dan Igbo ya zama shugaban kasa a 2023 shine abin da ya fi dacewa domin hakan zai samar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin yan kasar."

Kalu yana da halaye da suka sa ya cancanci zama shugaban kasa, Murtala

Shugaban na GMANN ya kuma yi bayanin cewa suna goyon bayan Kalu ne saboda yana da halaye da basira da zai iya jagorancin harkokin Najeriya kamar yadda Guardian ta ruwaito.

Ya kara da cewa tsohon gwamnan yana da basirar da zai iya kula da albarkatun kasar a wannan karnin na 21 duba da irin wayewarsa da gogewa a matsayinsa na dan kasuwa na duniya, tsohon gwamna kuma sanata.

Kara karanta wannan

An tara Malamai 2500 a Kano don addu'ar Allah ya ba Tinubu Shugabancin Najeriya

Mohammed ya cigaba da bayyana Kalu a matsayin mutum mai son 'demokradiyya, kuma mai jajircewa wurin kwato wa talaka hakkinsa sannan dan Najeriya mara nuna kabilanci, don haka za a amince da shi a duk sassan Najeriya da kasashen waje.'

Ya cigaba da cewa:

"Mun yi binciken mu, mun zabi Kalu a matsayin wanda muke ga ya dace ya gaji Shugaba Buhari a 2023 saboda wayewarsa, kwarewa da iya hada kan al'umma, daidaita harkokin kasa da samar da tsaro da cigaban tattalin arziki a karni ta 21."

Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa

A wani labarin, gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta san abun yi don kawo karshen rashin tsaro cikin watanni 17 – Gwamnan APC

Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel