Dan majalisar Kano ya bayyana mutum daya rak da ya cancanci darewa kujerar Buhari a 2023

Dan majalisar Kano ya bayyana mutum daya rak da ya cancanci darewa kujerar Buhari a 2023

  • Dan majalisar Kano mai wakiltan mazabar Tarauni a majalisar wakilai, Hafiz Kawu ya nuna goyon bayansa ga mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo don ya gaji Buhari
  • Kawu ya bayyana cewa Osinbajo ya cancanci zama shugaban kasa na gaba saboda biyayyarsa, iya aiki da kuma gogewarsa
  • Ya ce duk da cewar ya yi aiki a matsayin mukaddashin shugaban kasa a lokuta daban-daban, ba a taba jin kansa da ubangidan nasa ba

Kano - Gabannin zaben 2023, wani dan majalisar Kano mai wakiltan mazabar Tarauni a majalisar wakilai, Hafiz Kawu ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya cancanci darewa kujerar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kawu ya bayyana cewa Osinbajo ya cancanci ya gaji Buhari a matsayin shugaban kasa na gaba bisa ka'idojin shari'a, biyayyarsa da kuma ci gaba da aiwatar da ayyukan da gwamnatin ta fara da dai sauransu.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar arewa ta bayyana sanata daga kudu da ta ke son ya gaji Buhari

Dan majalisar Kano ya bayyana mutum daya rak da ya cancanci darewa kujerar Buhari a 2023
Dan majalisar Kano ya bayyana mutum daya rak da ya cancanci darewa kujerar Buhari a 2023 Hoto: Leadership
Asali: UGC

Dan majalisar ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano kan harkokin siyasa da ci gaban kasar, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce Osinbajo ya tabbatar da cancantarsa ta hanyar nuna bajinta a matsayin mukaddashin shugaban kasa lokuta da dama da kuma sauke hakkokin da aka daura masa cikin kwarewa.

Ya kuma ce hakan ya nuna cewa zai yi bajinta idan har ya zama magajin shugaban kasa Buhari.

Kawu ya ce:

"Idan kuna bibiyar abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan, daya daga cikin tsoffin shugabannin Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a kwanan nan ya nuna goyon bayansa ga mataimakin shugaban kasar a lokacin da ya karbi kungiyar matasan Najeriya da ke yakin neman zaben Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin shugaban kasa na gaba.

Kara karanta wannan

Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022

"Ya jinjina wa mataimakin shugaban kasar a matsayin mutumin kirki, don haka idan ka kalli abun ta wannan bangare, mutumin da ya cancanci ya gaji Shugaba Buhari shine Farfesa Osinbajo saboda shine mataimakin shugaban kasa kuma yana da kwarewa, iya aiki, halaye da gogewar da ake bukata don darewa kujerar Muhammadu Buhari.
"A iya sanina, Bola Tinubu bai ayyana aniyarsa ta takarar shugaban kasa ba kuma kasancewana daya daga cikin makusantar mataimakin shugaban kasar, na yi aiki a matsayin hadiminsa tsakanin 2015 da 2019 kafin na koma majalisar wakilai. Na san shi sosai, na san abun da zai iya don haka kamar yadda na fadi, a wannan lokaci da mutane ke cewa a mika mulki zuwa kudu, shine ya kamata ya gaji Muhammadu Buhari.
"Osinbajo ya kasance mai biyayya ga shugaban kasar, babu wanda zai ce ya ji labarin gaba tsakaninsa da ubangidansa a Najeriya kuma ya sha aiki a matsayin mukaddashin shugaban kasa lokacin da shugaban kasar yayi tafiya kuma ya nuna kwarewa wanda za a iya tuna wasu daga cikin abubuwan da yayi.

Kara karanta wannan

Kukah: Duk da yawan sukar da na ke yi wa gwamnatinsa, Buhari bai dena daukan waya na ba

"Hakazalika, za ku iya cewa ya yi shugaban kasa, kuma mukaddashin shugaban kasa tamkar shugaban kasa, don haka kun gan shi, kun ga abun da yayi, shi farfesan shari'a ne, bawan Allah kuma mutum da ya damu da matasan kasar nan sosai.
"Da nayi aiki a karkashin ofishinsa, mafi akasarinmu matasa ne tsakanin shekaru 40, ina ganin mafi yawan shekaru shine 60, ya yarda da Najeriya sosai, ya yarda da matasan Najeriya kamar yadda na fadi, shi jagora ne nagari."

Mista Kawu, wanda ya yaba wa shugaba Buhari kan kaddamar da manyan ayyuka a yankunan kasar, ya ce idan aka ba shi dama, Osinbajo zai kammala dukkan ayyukan da ake gudanarwa tare da kaddamar da wasu sabbi, Premium Times ta rahoto.

An tara Malamai 2500 a Kano don addu'ar Allah ya ba Tinubu Shugabancin Najeriya

A wani labarin kuma, mun ji cewa, Hanarabul Abdulmumin Jibrin Kofa ya shirya addu'o'i na musamman domin samun nasarar takarar Bola Tunubu a zaben shugaban kasa a 2023 da kuma zaman lafiya da hadin kai a Najeriya.

Kara karanta wannan

Buhari ya nada Karebo Samson a matsayin mukaddashin kwanturola Janar na hukumar kashe gobara

Tsohon dan majalisar wakilai wanda ya wakilcimazabar Kiru/Bebeji na tarayya, ya shirya wannan taron addu'a ne a jihar Kano ranar Asabar, 1 ga watan Junairu, 2022.

A lokacin da yake jawabi ga manema labarai, a gidansa dake Kofa, karamar hukumar Bebeji a jihar Kano, ya ce ya kirawo malamai 2,500 domin yi wa kasar nan addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu addu’a dangane da takarar shugaban kasa da zai yi a babban zabe na shekarar 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel