Jigon APC ya yaba da aikin Buni, ya ba da shawara kan shirin zaben 2023 ga Buhari

Jigon APC ya yaba da aikin Buni, ya ba da shawara kan shirin zaben 2023 ga Buhari

  • Wani jigon jam'iyyar APC ya bayyana bukatar yin gyara a jam'iyyar kafin zaben shekarar 2023 ya karasa zuwa
  • Hon. Patrick Obahiagbon ya bayyana haka ne a Abuja cikin wata wasikar da ya aikewa gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni
  • Ya ce Mai Mala Buni ya yi kokarin tabbatar da tafiyar jam'iyyar APC akan turba ta gari da jajircewa

Abuja - Jigon jam'iyyar APC, Hon. Patrick Obahiagbon ya shawarci shugaba Buhari da shugaban kwamitin shirya taron gangamin APC Mai Mala Buni kan shirya hanya dodar ga zaben 2023.

Hon Obahiagbon, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne ya yi wannan batu ne a ranar Litinin a Abuja, a wata wasikar yabo ga Mai Mala Buni, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya fara shirye-shiryen tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Jam'iyyar APC na shirin zaben 2023
Ya kamata Buhari ya share hanyar APC dodar a zaben 2023, inji jigon APC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Tsohon dan majalisar ya kara da cewa kada muradin kashin kai da son kai su wuce muradun jam’iyyar.

Hakazalika, ya koka kan yadda jam'iyyar ke fuskantar barazana da rikice-rikicen cikin gida, lamarin da yace ya kamata a kawo karshensa.

A bangare guda, ya bayyana ra'ayinsa da cewa, Mai Maka Buni ya dawo da jam'iyyar APC kan turba, duk da samun rikice-rikice daga mambobin jam'iyyar bambanta a baya, kamar yadda BluePrint ta tattaro.

Hon Obahiagbon ya ce salon jagoranci mai ban sha'awa da tsarin tuntuba daga Buni baya ga tawali'u, hadin kai tare da matsayi da kuma kwarewar hulda tsakanin mutane ya haifar da mai ido ga jam'iyyar.

Ministan Buhari ya bayyana sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

A wani labarin na daban, mambobin jam'iyyar APC a jihar Anambra, sun bukaci ministan kwadugo, Dakta Chris Ngige, ya nemi takarar shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Shekaru kadan bayan nada shi sarauta, fitaccen basarake ya riga mu gidan gaskiya

Daily Trust ta rahoto cewa akwai yuwuwar APC ta kai tikitin takara yankin kudu maso gabas, saboda haka mambobin jam'iyya a jihar ke ganin ya dace ministan ya yi amfani da wannan damar.

Mambobin jam'iyar sun fara bayyana ra'ayoyin su game da takarar ministan a mahaifarsa, Alor, ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel