Ajandar Talakawa 2023-2027: Shehu Sani ya bayyana abubuwa 12 da yake son cimma idan ya zama gwamna

Ajandar Talakawa 2023-2027: Shehu Sani ya bayyana abubuwa 12 da yake son cimma idan ya zama gwamna

  • Sanata Shehu Sani ya bayyana manyan abubuwan da zai yi wa talakawa idan har mafarkinsa na son zama gwamnan jihar Kaduna ya zama gaskiya
  • Daga cikin manyan ayyukan da tsohon sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya yayi alkawarin yi akwai kawo karshen ta'addanci, hadakan mutanen jihar da sauransu
  • Sani dai ya nuna sha’awarsa ta shiga jerin 'yan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a zaben 2023 mai zuwa a badi

Kaduna - Sanata Shehu Sani ya bayyana muhimman abubuwan da zai yi wa al'umman Kaduna idan har yayi nasarar zama gwamnan jihar a zaben 2023 mai zuwa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook wanda ya yi wa lakabi da 'Ajandar Talakawa na jihar Kaduna 2023-2027', Sani ya lissafa wasu abubuwa 12 da zai magance da zaran ya samu darewa kujerar gwamnan.

Kara karanta wannan

Yari, Modu Sheriff, Al-Makura da jerin mutum 10 masu harin shugabancin APC a zaben 2022

Ajandar Talakawa 2023-2027: Shehu Sani ya bayyana abubuwa 12 da yake son cimma idan ya zama gwamna
Ajandar Talakawa 2023-2027: Shehu Sani ya bayyana abubuwa 12 da yake son cimma idan ya zama gwamna
Asali: UGC

Tsohon sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci da ya addabi jihar tare da kare dukiyoyi da rayukan al'umma.

Ya wallafa a shafin nasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ajandana na Talakawa ga jihar Kaduna 2023-2027
1. Kawo karshen ’yan fashi da ta’addanci da kuma kare rayukan al’ummarmu ta hanyar ba da goyon baya ga dukkan hukumomin tsaro da ke jihar.
2. Hada kan mutane arewaci da kudancin Kaduna don zaman lafiyta, daidaito, adalci da ci gaba.
3. Tantancewa da biyan bashin da yayiwa jihar katutu.
4. Dawo da masana'antun jihar, sake farfado da masana'antun da suka mutu da kuma bayar da gagarumin tallafi ga kanana da matsakaitan sana'o'i.
5. Samar da ababen more rayuwa na yankunan karkara da aka yi watsi da su.
6. Soke kudade na fili da boye da kuma kudaden da ake biya a makarantun gwamnati da asibitocin gwamnati.

Kara karanta wannan

Aiki ga mai yin ka: El-Rufai ya sanar da mataki 1 tak na magance 'yan bindiga

7. Samar da gagarumin shiri na aikin noma da injina da masana'antun da ke da alaka da aikin gona domin bunkasa aikin gona na jihar.
8. Kafa sabbin jami'o'i biyu na likitanci, Injiniya da fasahar sadarwa.
9. Ceto bangaren wasanni da sake mayar da Kaduna ga manyan wasanni a kasar.
10. Hada kai da tallafawa kungiyoyin addini da cibiyoyin gargajiya don samar da tsaro, zaman lafiya da ci gaba.
11. Katafaren gine-ginen gidaje da samar da manyan birane a Zaria,Kafanchan da Kaduna.
12. Na bar wa kaina sanin sauran muhimman abubuwan da zanyi a yanzu.
"INSHA ALLAH"

Daga karshe: Shehu Sani ya bayyana aniyar tsayawa takarar gwamna, ya fadi manufarsa

A baya mun kawo cewa Sanata Shehu Sani ya nuna sha’awarsa ta shiga jerin 'yan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a zaben 2023 mai zuwa a badi, Daily Trust ta rahoto.

Tsohon sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan rediyon Invicta FM.

Kara karanta wannan

Shugabanci ba na mashiririta da zaman kashe wando bane, APC ta yi wa Shehu Sani martani

A cikin wani rufa-rufa da ya yi kan Gwamna Nasir El-Rufai, ya ce duk wanda ke zagi da cin mutuncin jama’a bai cancanci ya hau mulki ba saboda girmama dan Adam na da matukar muhimmanci a addini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel