Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

  • Kungiyar matan Arewa sun tabbatar wa gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi goyon bayan su a babban zaben 2023
  • Matan karkashin kungiyar YBN sun bayyana cewa gwamna Bello ya nuna zai iya jagorancin Najeriya duba da nasarorinsa a Kogi
  • A cewarsu, gwamnan yana tafiya da matasa da mata a harkar mulkinsa, kuma abin da yan Najeriya ke son gani kenan a matakin kasa

Abuja - Mata daga jihohin Arewa 19 sun bayyana goyon bayansu ga gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, a matsayin zabin su na shugaban ƙasa a 2023, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Tawagar matan karkashin kungiyar Yahaya Bello Network (YBN), sun faɗi haka ne yayin da suka kai wa Bello ziyara a gidan gwamnan Kogi dake Abuja.

Kara karanta wannan

Yari, Modu Sheriff, Al-Makura da jerin mutum 10 masu harin shugabancin APC a zaben 2022

Shugabar YBN, Honorabul Hadiza Ahmed, tace daga cikin yan siyasan da suka bayyana sha'awar ɗarewa kujerar shugaban ƙasa, Yahaya Bello ne zabin su duba da nasarorin da ya samu a Kogi.

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi
Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023 Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Hadiza tace dumbin nasarorin da Bello ya samu a matsayin gwamnan Kogi, ya sa ya zama wanda ya fi kowa dacewa ya gaji shugaba Buhari a zaben 2023.

A cewarta, waɗan nan nasarorin suka ja ra'ayoyin yan Najeriya da dama har da YBN suke rokonsa ya taimaka ya nemi takarar shugaban ƙasa.

Ta ƙara da cewa Bello ya nuna kyakkyawan jagoranci a jihar Kogi, wanda idan mutum ya duba zai ga haka a kowane ɓangaren jihar.

YBN ta yaba wa gwamnan tare da rokon ya amsa kiran yan Najeriya

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar arewa ta bayyana sanata daga kudu da ta ke son ya gaji Buhari

Daga nan kuma, shugabar YBN ta yaba wa gwamnan bisa yadda ya maida matasa da mata tamkar abokansa ta hanyar jawo su a gwamnatinsa, wanda a cewarta ya jawo masa suna a ƙasa da ƙasa.

Honorabul Hadiza tace:

"Mun zo nan ne mu mika kokon baran mu ga mai girma zababben gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya amsa kiran mu matasa ya fito takarar shugaban ƙasa a 2023."
"Gwamnatinsa ta jawo matasa da mata ta ba su mukamai, wanda hakan muke son gani a matakin ƙasa sabida matasa yan Najeriya ke fatan su karbi kasar nan a 2023."
"Ka riga ka nuna misali a jihar Kogi kuma muna da tabbacin zaka sake kwatanta haka idan ka zamo shugaban ƙasa."

A wani labarin na daban kuma Khadijat yar kimanin shekara 38 ta bayyana shirinta na maye gurbin shugaba Buhari a zaɓen 2023

A tarihin Najeriya ba'a taba samun mace da ta zama shugaban ƙasa ba tun bayan samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka a shekarar 1960.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi watsi da Tinubu, Atiku da Saraki, ya faɗi wanda yan Najeriya za su zaba a 2023

Wata matashiya yar shekara 38, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta bayyana sha'awarta na maye gurbin shugaba Buhari a babban zaben 2023 dake tafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel