Siyasar Najeriya
Awanni gabanin zaben tantance wanda ya ci gwamna a jihar Kebbi, jam'iyyar APC ta dakatar da ɗan majalisar tarayya, Honorabul Shehu Muhammed Koko, kan zargi.
Jam'iyyar APC ta yi karin haske game da shirye-shiryen karban mulki duk da shugaban kasa mai jiran gado ya bar Najeriya domin ya ɗan sarara a nahiyar Turai.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya nemi masu kaɗa kuri'a su dangwalawa jam'iyyar PDP a cikon zaben jihohin Adamawa da Kebbi gobe Asabar.
Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a Kano ta fada wa kotun sauraron kararrakin zabe cewa Abba Kabir Yusuf na NNPP kuri'a 178,378 ya samu ba miliyan ba.
Shugabancin Majalisar Wakilan zai iya fadawa Arewa, Franic Waice yana neman Mataimaki. Waice ya roki a zabe shi ya zama mataimakin Shugaban Majalisar kasar.
Yayin da ake tunkarar sabuwar gwamnati karkashin Bola Ahmed Tinubu, mun tattara muku Sanatocin Arewa 5 da suka shiga tseren zama shugaban majalisar dattawa.
Ƴan majalisa da dama sun shiga cikin tseren neman shugabancin majalisar dattawa ta 10. Ƴan majalisar dattawan sun fito ne daga yankuna daban-daban na ƙasar nan.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya tabbatar da shirinsa na neman tazarce kan kujerarsa karkashin inuwar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Imo.mai zuwa.
Bayan zargin hannu a aikata ta'addanci da gwamna Yahaya Bello ya musu, shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki, Murktar Bajeh, ya yi murabus, an naɗa sabo.
Siyasar Najeriya
Samu kari