Bayanai Sun Fito Kan Ganawar Shugaba Tinubu, Dangote da Matawalle a Villa

Bayanai Sun Fito Kan Ganawar Shugaba Tinubu, Dangote da Matawalle a Villa

  • Yayin da Bola Ahmad Tinubu, Shugaban kasar Najeriya ya gana da Dangote da Matawalle, bayanai sun fito
  • Matawalle ya ce yana da yakinin Tinubu zai cika dukkan alkawuran da ya dauka na kamfen nan ba da jimawa ba
  • Tinubu ya fara mulkinsa ne ta hanyar fara daukar tsauraran matakan da suka ba 'yan kasar nan mamaki, ciki har da janye tallafin man fetur

FCT, Abuja - A ranar Juma’ar da ta gabata ne Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya karbi bakuncin Shugaban Rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote a fadar Shugaban kasa ta Villa da ke Abuja, rahoton Daily Sun.

Dangote bai yi magana da ‘yan jarida a Villa ba kan manufar ganawar, ya kuma ce zai sake kawai irin wannan ziyarar a mako mai zuwa tare da shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates, Mista Bill Gates.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Ɗangote da Tsohon Gwamnan Zamfara a Villa, Ya Yi Jawabi Mai Jan Hankali

Haka kuma, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, ya ziyarci shugaba Tinubu a ofishinsa da ke Villa a ranar ta Juma'a, The Nation ta ruwaito.

Ganawar Tinubu da Matawalle; bayanai sun fito
Bola Ahmad Tinubu, Shugaban kasar Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Dalilin ganawar Tinubu da jiga-jigan

Matawalle, ya ce ziyarar da ya kai wa Tinubu ta da ne ga uba, ya kuma yi nuni da cewa, shugaban kasar yana ta kokarin gamsar da duniya cewa yana da zakamin jagorancin kasar nan daidai kuma yana ganin zai zama shugaban kasa mafi alheri da Najeriya ta taba samu. .

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Matawalle:

“Ya zuwa yanzu dai kun ga yadda Shugaban kasa ya fara aiki, wannan ba sabon abu ba ne a gare shi, shi ma’aikaci ne na gari, mai kyawawan manufofi. Zai cika dukkan alkawuran yakin neman zabensa.
“Da ganin yadda ya fara mulkinsa, mutane da yawa sun fara aminta cewa Najeriya za ta zama kasa mafi kyau a yankin nans. Mun yi imanin cewa Asiwaju zai zama shugaban kasa mafi kyau da Najeriya ta taba samu."

Kara karanta wannan

Dangote, Bill Gates Za Su Gana Da Tinubu A Ranar Litinin

'Yan Najeriya sun yi sallama da tallafin man fetur, cewar Tinubu

A ranar da ya karbi mulkin kasar nan, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana janye tallafin man fetur gaba dayansa.

Wannan ya faru ne sakamakon kudaden da ake kashewa a fannin mai da kuma rashin tasirin hakan ga tattalin arziki.

A cewar shugaban, hakan zai ba Najeriya daman mai da kudaden tallafin kan manyan ayyukan da za su amfani kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel