Gudaji Kazaure: Jerin Ministoci Da Mukarraban Buhari Da Ya Kamata Tinubu Ya Kamo Su Yi Bayani

Gudaji Kazaure: Jerin Ministoci Da Mukarraban Buhari Da Ya Kamata Tinubu Ya Kamo Su Yi Bayani

Tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Jigawa, Muhammed Gudaji Kazaure, ya bankaɗo sunayen manyan jiga-jigan da ya kamata a cafke a Najeriya.

A cikin wani shirin Berekete Family da ake haskawa a Talabijin, Gudaji Kazaure, ya ce matuƙar dagaske ana son farfaɗo da tattalin arziki, ya kamata shugaba Bola Tinubu, ya sa a kama waɗan nan mutanen.

Shugaba Tinubu da Gudaji Kazaure.
Jerin Ministoci da Mukarraban Buhari Da Ya Kamata Tinubu Ya Kamo Su Yi Bayani Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tsohon ɗan majalisar ya ambaci sunayen tsoffin monistoci, gwamnonin CBN da shugabannin hukumomin tattara haraji a zamanin mulkin Muhammadu Buhari.

Jerin sunayen mutanen da Kazaure ya lissafa

Legit.ng Hausa ta tattaro muku sunayen da Gudaji Kazaure ya ambata da kuma dalilansa, ga su kamar haka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, wanda yanzu haka yana hannun DSS.

Kara karanta wannan

Bashin N187bn: Hukumar EFCC Ta Tsare Tsohon Gwamnan Arewa Na PDP, Bayanai Sun Fito

2. Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa

Duk da Bawa na hannun jami'an tsaron farin kaya DSS, Kazaure ya ce yayin bincikarsa ya kamata a gayyato tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya yi bayani kan abinda ya bari.

3. Shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari

4. Tsohon ministan shari'a kuma tsohon Antoni Janar, Abubakar Malami.

5. Sakataren kai da kai na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau Sabi'u Tunde.

6. Shugaban hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS), Muhammad Nami.

7. Darakta Janar na hukumar NIMASA, Bashir Yusuf Jamoh (Ph.D).

8. Shugaban hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa (NPA), Mohammed Bello Koko.

Dangane da wannan, Honorabul Kazaure, ya ce bayan cafke Koko, ya kamata a gayyato tsohuwar shugabar NPA, Hadiza Bala Usman, ita ma ta yi bayani dalla-dalla.

9. Baki ɗaya mataimakan gwamnan CBN na yanzu, waɗanda suka yi aiki da Emefiele. A cewarsa akwai buƙatar su faɗi duk wani abinda suka sani a zamanin Emefiele.

Kara karanta wannan

PDP Ta Shiga Tangal-Tangal, Shugabanni 7 da Suka Yi Murabus Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

10. Tsohuwar ministar jin kai da walaha, Hajiya Sadiya Umar Farouq da muƙarrabanta.

11. Kafatanin shugabannin hukumar NIBSS.

Gudaji ya ƙara da cewa shugabannin NIBSS (Nigeria Inter-Bank Settlement System) ne kaɗai zasu iya bayanin inda kuɗin da ake cajin mutane a Banki suka sulale.

Ya yi zargin cewa wani Asusu suka kirkira, inda suke zuba kuɗin bayan sun ɗan tura wa asusum gwamnatin tarayya. Ya ce duk kuɗin Stamp Duty na wurinsu.

Kalli bidiyon kalaman Gudaji Kazaure

Shugaba Bola Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri da Asari Dakubo a Aso Villa

A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sa labule da Asari Dakubo a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

Dakubo ya isa fadar shugaban ƙasa da karfe 11:00 na safiyar ranar Jumu'a kuma daga zuwa ya shiga ganawar sirri da Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262