Shugaba Tinubu Ya Kara Wa Nuhu Ribadu Girma Zuwa Bai Bada Shawara Kan Tsaron Kasa

Shugaba Tinubu Ya Kara Wa Nuhu Ribadu Girma Zuwa Bai Bada Shawara Kan Tsaron Kasa

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Nuhu Ribadu karin girma daga mashawarci na musamman kan tsaro zuwa mai bada shawara kan tsaro na kasa
  • Shugaban kasar ya bada wannan sanarwar ne tare da naddin sabbin hafsoshin tsaro, ciki har da shugaban hafsan sojojin kasa da na tsaro
  • Sanarwar nadin Nuhu Ribadu a matsayin NSA ya kawo karshen cece-kuce da ake yi bisa nadinsa na farko

Aso Villa, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya kara wa Nuhu Ribadu girma daga Mashawarci Na Musamman Kan Tsaro zuwa Mai Bada Shawara Kan Tsaron Kasa.

Idan za a iya tuna wa Shugaban kasar ya sanar da shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC din a matsayin mashawarci na musamman kan tsaro a satin da ta gabata, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ribadu: Muhimman Abubuwa 7 Da Baku Sani Ba Game Da Sabon Mai Ba Da Shawara A Harkokin Tsaro

Tinubu ya nada Nuhu Ribadu a matsayin NSA
Tinubu Ya Kara Wa Nuhu Ribadu Girma Zuwa Bai Bada Shawara Kan Tsaron Kasa. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Yadda Tinubu ya kara wa Ribadu girma

Amma, a wani cigaba da aka samu a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, Tinubu ya sallami dukkan shugabannin hukumomin tsaro ciki har da mai bada shawara kan tsaro na kasa, kuma ya sanar da Ribadu a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, Tinubu ya sanar da Ribadu a matsayin mashawarci na musamman kan tsaro tare da wasu mashawarta na musamman guda bakwai amma sanarwar ta haifar da cece-kuce tsakanin masu sharhi kan harkokin siyasa da ke kokarin banbance aikin Ribadu da na Mai Bada Shawara Kan Tsaron Kasa.

Amma, shugaban kasar cikin wani sabon mataki a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, ya sanar da nadin Ribadu a matsayin Mai Bada Shawara Kan Tsaron Kasa tare da sauran shugabannin hafsoshin tsaro.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Bola Tinubu: Cikakkun Sunayen Hafsoshin Tsaro, Manyan Kwamandojin Fadar Shugaban Kasa Da Sauransu

Takaitaccen tarihin Ribadu kafin Tinubu ya nada shi

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fara nada tsohon mataimakin sifeta janar na yan sandan, Nuhu Ribadu a matsayin shugaban Hukumar Yaki da Rashawa, EFCC.

Nadin da Tinubu ya yi wa Ribadu zai fara aiki ne nan take.

Mutane suna ta maganganu kan Shugaba Tinubu tun ranar farko da ya karbi mulki lokacin da ya sanar da cire tallafin man fetur.

Ya kuma yi wasu maganganu kan tsare-tsare da ilimi kuma ya dakatar da shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa da gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele.

Tinubu zai kai ziyara Faransa

Tunda farko kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu zai kai ziyarar farko kasar waje a matsayinsa na shugaban kasa zuwa Faransa.

Tinubu zai shafe kwanaki biyu ne a Faransan kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel