Tashin Hankali Yayin da Aka Kashe Dan Sanda a Lokacin Da ’Yan Bindiga Suka Kai Wa Ayarin Okorocha Hari

Tashin Hankali Yayin da Aka Kashe Dan Sanda a Lokacin Da ’Yan Bindiga Suka Kai Wa Ayarin Okorocha Hari

  • Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani jami’in dan sanda
  • Okorocha ya nuna fushinsa da rashin jin dadin game da harin, inda ya nuna bambancin tsaro da ya samu a Enugu
  • Tsohon gwamnan na Imo ya soki yanayin da jiharsa ke ciki, ya kuma yi ishara tare da yin magana kan dan takarar da zai mara ma baya a zaben gwamna mai zuwa.

Jihar EnuguA ranar Juma’a, 16 ga watan Yuni, ‘yan bindiga suka kai hari kan ayarin motocin tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, inda suka yi sanadin mutuwar wani jami’in dan sanda.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa an kai masa harin ne a unguwar Ihube da ke kan hanyar Okigwe zuwa Enugu.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamna Zai Ba Mazauna Garuruwa Makamai Domin Yakar ‘Yan Bindiga a Arewa

An farmaki ayarin Okorocha
Tsohon gwamnan Imo da aka farmaki ayarinsa | Hoto: Senator Rochas Okorocha
Asali: Facebook

Yadda aka kaiwa ayarina hari, daga balin Okorocha

Okorocha ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da nuna alhininsa kan harin da aka kai wa ayarin motocinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa dan sandan da aka kashe yana cikin tawagar jami’an tsaro da gidan gwamnatin jihar Enugu ta bas hi domin su raka shi wajen bikin jana’izar mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha.

Da yake jawabi a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna mai zuwa a Imo, Samuel Anyanwu, Okorocha ya bayyana kashe jami’in a matsayin babban abin takaici.

Ya bayyana cewa yana dawowa daga Enugu, inda ya halarci bikin binne matar tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani lokacin da aka farmake shi.

Okorocha ya kara da cewa gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya samar masa da motoci da jami’an tsaro domin raka shi zuwa jihar Imo, rahoton jaridar Ripples Nigeria.

Kara karanta wannan

An Zabo Mana Bala'i: Kanawa Sun Fusata Da Rushe-Rushen Abba, Sun Hana Rushe Gidajensu

Na yi kwana biyu a Enugu babu abin da ya faru dani, inji Okorocha

Da yake bayyana bacin ransa, Okorocha ya jaddada bambancin da ke tsakanin zamansa lafiya a Enugu da kuma harin da aka kai masa jiharsa, wanda ya yi sanadin rasa ran jami’in tsaro.

Ya soki yadda al’amura ke lalacewa a Imo, inda ya bayyana rashin gamsuwarsa da masu neman gwamna a jihar.

Sai dai, ya ware mutum daya tare da bayyana yabo ga halayensa da yadda yake gudanar da lamuransa.

Daga karshe, Okorocha ya sha alwashin magance lamarin a lokacin da ya dace idan ya samu dama.

Ba wannan ne karon farko da ake farmakar masu rike da mukamai ba, an sha yin hakan a Najeriya a lokuta mabambanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel