Koda Ka Koma Jam'iyyar APC, Kar Ka Yi Nesa Da Ni, Gwamna Fubara

Koda Ka Koma Jam'iyyar APC, Kar Ka Yi Nesa Da Ni, Gwamna Fubara

  • Gwamnan jihar Ribas ya roki tsohon gwamnan da ya karɓa daga hannunsa, Nyesom Wike, kar ya yi nesa da shi
  • Siminalayi Fubara, ya ce alamu sun nuna Wike na yunkurin sauya sheka zuwa APC don haka ya nemi alfarma daga wurinsa
  • Wike, babban jigo a jam'iyyar adawa PDP ya kai ziyara fadar shugaban ƙasa Tinubu a lokuta da dama bayan 29 ga watan Mayu

Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya roƙi magabacinsa, Nyesom Wike, alfarmar cewa kar ya yi nesa da shi koda ya yanke shawarin sauya sheka zuwa APC.

Daily Trust ta rahoto cewa Wike na ɗasawa da jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki tun bayan lokacin da ya rasa tikitin takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa a inuwar PDP.

Gwamnan Ribas tare da Nyesom Wike.
Koda Ka Koma Jam'iyyar APC, Kar Ka Yi Nesa Da Ni, Gwamna Fubara Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ne ya lallasa Wike a zaɓen fidda gwanin PDP daga bisani kuma ya ɗauki tsohon gwamna Ifeanyi Okowa na Delta a matsayin abokin takararsa.

Kara karanta wannan

Sabon Rahoto Ya Bayyana Matsayin Da Ake Sa Ran Tinubu Zai Ba Kwankwaso A Majalisar Ministocinsa

A lokacin da ake cikin kakar babban zaɓen 2023, Nyesom Wike da masu mara masa baya suka tsame hannunsu daga tawagar yaƙin neman zaɓen Alhaji Atiku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tinubu ya jinjinawa Wike

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya fahimci girman taimakon da Wike ya masa kana ya jinjina masa, an ji yana cewa ba dan Wike ba, ba zai ci zaɓen shugaban ƙasa ba.

A rahoton Punch, Tun da Tinubu ya karɓi mulkin Najeriya a karshen watan Mayu, an ga Wike a lokuta da dama ya ziyarci fadar shugaban kasa tare da wasu masu faɗa aji a APC.

Wannan yasa a ka ci gaba da yaɗa raɗe-raɗin cewa Wike na shirye-shiryen komawa jam'iyyar APC, amma duk da haka tsohon gwamnan ya ce ba gaskiya bane.

Kada ka yi nesa da ni idan ka koma APC - Fubara ga Wike

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Bayyana Hukuncin Da Ya Cancanci PDP Ta Yi Wa Wike Kan Cin Dunduniyarta Da Ta Atiku

Da yake jawabi a wurin taron liyafar godiya da aka shirya domin girmama Wike, Gwamna Fubara na jihar Ribas, ya ce:

"Yayin da muka ga alamar kana son tsallakawa zuwa ɗaya bangaren tare da mutane na fatan haka, Dan Allah kada ka yi nesa da ni saboda kifayen nan da damisoshi na nan a laɓe, suna jiran samun dama su cutar da ni."
"Kasancewarka a kusa da ni zai bani ƙarfin guiwa da karsashin zage dantse domin tabbatar da manufar jihar mu."

Jerin Ministoci da Mukarraban Buhari Da Ya Kamata Tinubu Ya Kamo Su Yi Bayani

A wani rahoton kuma Mun kawo muku jerin manyan kusoshin gwamnatin Buhari da ya kamata shugaba Tinubu ya kame su don fargaɗo da tattalin arziki.

Tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Jigawa, Muhammed Gudaji Kazaure, ne ya bankaɗo sunayen manyan jiga-jigan da ya kamata a cafke a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel