Dalilin da Ya Sa Na Marawa Akpabio Baya Har Ya Zama Shugaban Majalisa, Wike

Dalilin da Ya Sa Na Marawa Akpabio Baya Har Ya Zama Shugaban Majalisa, Wike

  • Nyesom Wike ya bayyana cewa ya mara wa Sanata Akpabio baya har ya zama shugaban majalisar dattawa ne saboda alherin da ya masa a baya
  • Tsohon gwamnan jihar Ribas ya ce sabon shugaban Sanatoci a majalisa ta 10 mai kaunarsa ne tun tale-tale
  • Ya ce lokacin da yake fafutukar neman zama gwamnan Ribas a 2014 da 2015 Akpabio ya tallafa masa da N200m

Rivers - Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana asalin dalilin da ya sa ya marawa Godswill Akpabio baya har ya samu nasarar zama shugaban majalisar dattawa ta 10.

Mista Wike ya ayyana Sanata Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom a matsayin mai goyon bayansa na tsawon lokaci, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Nyesom Wike.
Dalilin da Ya Sa Na Marawa Akpabio Baya Har Ya Zama Shugaban Majalisa, Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa lokacin da yake neman takarar gwamnan jihar Ribas a shekarar 2014 zuwa 2015, Akpabio ya tallafa masa da miliyan N200m na kamfe.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Faɗi Babban Jigon da Alamu Suka Nuna Zai Koma APC, Ya Roƙe Shi Alfarma 1

Wike ya yi wannan furucin ne a wurin taron liyafar da iyalansa suka shirya masa a Majami'ar St. Peters Deanery, Rumuepirikom, ƙaramar hukumar Obio-Akpor, ranar Lahadi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ƙara da cewa a daidai lokacin da ake ta sukarsa da nuna masa tsangwama, Akpabio kuwa ya maida hankali wajen mara masa baya ya zama gwamna a 2015.

"Loƙacin da nake neman takara a 2014 da 2015, shi ne mutum ɗaya da ya fito fili ya nuna mun goyon baya, ya bani kyautar miliyan N200 domin na tunkari zaɓe."
"Shiyasa a kowane lokaci nake yawan cewa wanda ya yi da kyau zai ga da kyau. A wannan karon ni na goyi bayansa kuma ina ƙara gode wa Allah tunda ya ba shi nasara."

- Nyesom Wike.

Akpabio ya maida martani

Kara karanta wannan

"Na Sha Da kyar": Wike Ya Bayyana Yadda Aka Zuba Masa Guba A Sakatariyar PDP A Abuja

Da yake martani kan haka, Sanata Akpabio ya ce miliyan N200m da ya lale ya bai wa tsohon gwamnan Ribas ba daga aljihun jihar Akwa Ibom ya ɗiba ba domin lokacin yana kujerar gwamna.

Sabon shugaban majalisar dattawan ya ce daga cikin kuɗin da ya tara ne lokacin yana daraktan kamfanin Sadarwa ya ɗebo ya bai wa Wike, kamar yadda Pulse ta tattaro.

Koda Ka Koma Jam'iyyar APC, Kar Ka Yi Nesa Da Ni, Gwamna Fubara

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Fubara ya roki Wike kar ya yi nesa da shi idan ya tsallaka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Siminalayi Fubara, ya ce alamu sun nuna Wike na yunkurin sauya sheka zuwa APC don haka ya nemi alfarma daga wurinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel