Siyasar Najeriya
Yayin da shekarar 2023 ke bankwana, wasu gwamnoni a Najeriya sun amince da bai wa ma'aikata kyautar N100,000 a jihohinsu domin bukukuwan kirsimeti.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga tsakani yayin da manyan ƴan siyasa a jihar Ondo suka fara faɗi tashin neman ɗarewa kujerar mataimakin Aiyedatiwa.
Sabuwar rigima ta ƙara ɓallewa a jam'iyyar Labour Party yayin da wasu shugabanni na tsagin Lamidi Apapa suka ci na jaki a jihar Edo ranar Jumu'a.
Shugabannin kananan hukumomin jihar Kano 44 sun nuna sam ba su yarda da yunkurin gwamnatin jihar Kano na talauta asusun baitul mali wajen gida gadoji ba.
Gwamnatin jihar Ekiti ta ayyana zamam makokin kwanaki 3 da sauke tutoci zuwa ɗabi domin nuna alhini da girmama marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo na ci gaba da laluben mutum mai tsantaar biyayya wanda zai masa mataimakin gwamna bayan rantsar da shi ranar Laraba.
Razaq Aderibigbe, jigon NNPP mai kayan marmari ya bayyana yaƙini cewa kotun kolin Najeriya zata tabbatar da adalci a shari'ar zaben gwamnan Kano da ke gabanta.
Primate Ayodele ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara zai ka.jam'iyyar APC nan gaba kaɗan domim ba zai iya jure faɗansa da ministan Abuja, Nyesom Wike ba.
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya zama mutum na farko da ya fara biyan albashin wata 13 a shekara ɗaya ga ma'aikatan gwamnati a tarihin jihar.
Siyasar Najeriya
Samu kari