Majalisar Dattawa Ta Hana Sabbin Sanatoci Tsayawa Takarar Shugabancin Majalisar

Majalisar Dattawa Ta Hana Sabbin Sanatoci Tsayawa Takarar Shugabancin Majalisar

  • Majalisar dattawan Najeriya a ƙarƙashin jagorancin Godswill Akpabio ta yi wa dokokinta garambawul domin gudanar da ayyukanta
  • A garambawul ɗin da majalisar ta yi, ta hana sabbin sanatoci yin takarar kujerar shugaban majalisa da mataimakinsa
  • Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele shi ne ya gabatar da wannan sabon kuɗirin a gaban majalisar

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta dakatar da sanatoci da suka zo majalisar a karon farko daga tsayawa takarar shugaban majalisar dattawa da mataimakin shugaban majalisar bayan da aka yi wa dokokinta gyaran fuska a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba.

Hakan dai na zuwa ne ƴan watanni bayan Sanata Abdulaziz Yari wanda ya taɓa yin ɗan majalisar wakilai, wanda yake karon farko a matsayin sanata, ya yi takara da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

Majalisar dattawa ta hana sabbin sanatoci tsayawa takara
Majalisar dattawa ta haramta takarar shugabancin majalisa ga sabbin sanatoci Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Ta hanyar yin gyaran fuska ga dokokin na majalisar dattawa, a yanzu an cire sanatoci wanda suke a wa'adi na farko daga cancanta ko cancantar shiga takarar shugabannin majalisar dattawa.

Wane sanata ne ga gabatar da ƙudirin?

Sanata Opeyemi Bamidele (Ekiti ta tsakiya, APC), shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa ne ya gabatar da ƙudirin gyara doka ta 3 (2) (1-3) ta majalisar dattawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Opeyemi ya yi wa ƙudirin taken:

"Garambawul ga dokokin majalisar dattawa bisa umarni na doka ta 109 ta majalisar dattawa, ta shekarar 2022 (wacce aka yi wa kwaskwarima)."

Kamar yadda aka yi mata kwaskwarima, doka ta 3 ta majalisar dattawan, ta ce duk wani Sanata da ke da sha'awar tsayawa takarar manyan muƙamai biyu na shugaban majalisar dattawa da mataimakin shugaban majalisa, sai ya kasance a majalisar na aƙalla wa'adi ɗaya.

Kara karanta wannan

Karin Albashin N35k Da Jerin Tallafin Da Shugaba Tinubu Ya Fito Da Su Bayan Cire Tallafin Man Fetur

Daga nan sai ta ƙara gyara dokokinta domin samar da wasu kwamitoci guda tara. A halin yanzu, majalisar tana da kwamitoci 74.

Tinubu Ya Aika Da Sabbin Ministoci Ga Majalisa

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da wasiƙa zuwa ga majalisar dattawa domin amincewa da ƙarin ministoci uku da ya naɗa.

Ɗaga cikin ƙarin ministocin akwai Balarabe Abbas wanda ya maye gurbin El-Rufai daga jihar Kaduna. Sauran sun haɗa da Dr. Jamila Bio da Olawale Olawande.

Asali: Legit.ng

Online view pixel