Kotun Zaben Kano: An Nemi DSS Da Yan Sanda Su Binciki Abba Gida Gida Kan Zanga-Zangar Landan

Kotun Zaben Kano: An Nemi DSS Da Yan Sanda Su Binciki Abba Gida Gida Kan Zanga-Zangar Landan

  • Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano da jam'iyyar NNPP sun sake shiga sabuwar matsala
  • Wasu magoya bayan NNPP da Abba gida gida sun gudanar da zanga-zangar adawa da bangaren shari'ar Najeriya a birnin Landan a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba
  • An zargi gwamnan Kano da aka tsige da shugabancin NNPP da daukar nauyin zanga-zangar na birnin Landan

FCT, Abuja - An caccaki Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano da jam'iyyar NNPP kan gudanar da zanga-zanga a birnin Landan a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba kan hukuncin alkalan kotun zaben gwamnan jihar.

Ku tuna cewa a ranar Laraba, 20 ga watan Satumba, kotun zaben ta ayyana dan takarar jam'iyyar APC, a zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris, Nasir Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zabe.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin Da Kotun Zabe Ta Tsige Cikin Wata 5 Da Dalili

An caccaki Abba Gida Gida kan zanga-zangar da yan NNPP suka yi a Landan
Kotun Zaben Kano: An Nemi DSS Da Yan Sanda Su Binciki Abba Gida Gida Kan Zanga-Zangar Landan Hoto: DSS/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A hukuncin kotun zaben, wanda aka gudanar ta yanar gizo, ta umurci hukumar zabe da ta soke takardar shaidar cin zaben da ta bai wa Gwamna Yusuf sannan ta mika shi ga Gawuna na APC.

A cikin wata sanarwa da aka gabatarwa jaridar Legit, kungiyar goyon bayan APC ta soki masu zanga-zangar na NNPP a Landan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi jam'iyyar NNPP da Gwamna Yusuf da daukar nauyin masu zanga-zangar na Landan kan bangaren shari'ar Najeriya lamarin da kungiyar ta APC ta bayyana a matsayin abun kunya.

Kotun zaben Kano: An bukaci DSS da yan sanda su binciki Abba gida gida

Yayin da take jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba, sakatariyar kungiyar ta kasa, Barista Isabella Odunayo, ya yi kira ga Sufeto Janar na yan sanda da hukumar DSS da su binciki Gwamna Yusuf da shugabancin NNPP kan zanga-zangar na Landan.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

Ta ce:

"Bayan rashin nasara a yunkurinta na bata hukuncin kotun zaben, tsananin son zuciyar NNPP ya kai su Landan inda ta dauki nauyin wani zanga-zanga don bata sunan gwamnatin tarayya da bata hukuncin kotun zaben...
"Abun kunya ne cewa Injiniya Abba Kabir Yusuf da kungiyar Kwankwasiyya sun samu mutane takwas ne kacal don gudanar da zanga-zanga wanda ake sa ran kimanin mutum dubu daya (1000) su hallara, wata alama da ke nuna cewa yan Najeriya na gida da waje sun yarda da hukuncin da zuciya daya.
"Muna kira ga sufeto janar na yan sanda da hukumar DSS da su fara gudanar da binciken Gwamnan jihar Kano mai barin gado Abba Kabir Yusuf da shugabancin NNPP gabannin hukunta su."

Jerin gwamnoni 2 da kotun zabe ta tsige cikin wata 5

A wani labarin, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnoni na 2023 a jihohi 28 da aka gudanar da zaben ranar 18 ga watan Maris ta tsige akalla gwamnoni biyu cikin wata biyar da rantsar da su.

Dokar zaben Najeriya ta bayar da damar da fusatattun jam'iyyu za su shigar da kara a kan jam'iyyar da ta yi nasara cikin kwanaki 21, kuma ana sa ran kotunan zaben su saurari shari'ar tare da yanke hukuncinsu kan kararrakin cikin kwanaki 180.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng