Gwamna Abdullahi Sule Zai Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun Zabe

Gwamna Abdullahi Sule Zai Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun Zabe

  • Gwamna Sule na jihar Nasarawa ya ce zai daukaka hukuncin da Kotun zabe ta yanke zuwa gaba domin kwato hakkinsa
  • Ya ce hukuncin wanda ya soke nasarar da ya samu, koma baya ne da zai dauki darasi daga ciki kana ya shirya fitowa da karfi
  • A ranar Litinin, Kotun zabe ta tsige Sule kuma ta ayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya ci zaben watan Maris

Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce zai daukaka kara kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke zamanta a Lafia ta yanke.

A ranar Litinin 2 ga watan Oktoba, Kotun ta soke nasarar da gwamna Sule ya samu, kana ta ayyana dan takarar PDP a matsayin sahihin zababben gwamnan Nasarawa.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.
Gwamna Abdullahi Sule Dam Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun Zabe Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Amma da yake martani kan wannan hukunci, Gwamna Sule ya lashi takobin dawo da nasarar da ya samu a Kotun daukaka kara, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin Da Kotun Zabe Ta Tsige Cikin Wata 5 Da Dalili

Ya ce hukuncin wani koma baya ne na wucin gadi wanda za su dauki darasi daga gare shi domin su sake yin wani tsari kuma su fito da karfin nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sule ya ce:

"Har yanzu ni zan ci gaba da zama gwamna har sai kotun koli ta yanke hukuncin da ya saba wa haka saboda doka ta ba ni damar daukaka kara kuma za mu yi hakan ne domin dawo da hakkinmu."

Kowa ya kwantar da hankalinsa - Sule

Gwamnan ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, kada su dauki doka a hannunsu ta hanyar yin zanga-zangar lumana a kan tituna.

Ya kuma gargadi matasa da magoya bayan jam’iyyar APC da su guji mayar da martani ga ‘yan adawa musamman a shafukan sada zumunta.

Kotun ta yanke hukuncin soke zaben gwamna Sule na jam’iyyar APC tare da bayyana Mista David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben na gaskiya.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

Mai shari’a Ezekiel Ajayi, shugaban kwamitin alkalan kotun ne ya karanta mafi akasarin hukuncin jiya Litinin, kamar yadda jaridar Pulse ta ruwaito.

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jiha Adamawa

A wani rahoton na daban Kotun zabe ta kori karar jam'iyya SDP da dan takararta, ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa

Sai dai har yanzu Kotun ba ta yanke hukunci kan karar da Aishatu Binani ta jam'iyyar APC ta shigar kan zaben ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel