Jigon APC Shinkafi Ya Caccaki Gwamnan Zamfara Kan Zargin FG da Tattaunawa Da ’Yan Bindiga

Jigon APC Shinkafi Ya Caccaki Gwamnan Zamfara Kan Zargin FG da Tattaunawa Da ’Yan Bindiga

  • Jigon APC kuma mai fada a ji a fannin tsaro a jihar Zamfara ya bayyana rashin jin dadinsa ga yadda gwamnan jihar ya zargi gwamnati ta tattaunawa da ‘yan bindiga
  • Ya bayyana cewa, akwai yiwuwar gwamnan jihar na neman suna ne ta hanyar kawo rudu a lamarin da ya shafi tsaron jihar da ke Arewa maso Yamma
  • Zamfara da jihohin da ke zagaye da ita a shiyyar na yawan fuskantar hari da barnar ‘yan bindiga a shekarun nan, musamman a mulkin da ya gabata

Jihar Zamfara - Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Dr Sani Shinkafi, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi watsi da batun gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal a kalaman da ya yi kan ganawar sirrin da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Dole za ku sha wahala: Tinubu ya ce 'yan Najeriya su shirya shan kebura, gyara babu dadi

An caccaki gwamnan Zamfara
Dauda Lawal ya sha sukar jigon APC | Hoto: Dauda Lawal, Dr Sani Shinkafi
Asali: Facebook

Shinkafi ya bayyana cewa:

“Abin takaici ne yadda Gwamna Lawal zai nemi suna ta hanyar wasa da rayuwar jama’a a daidai lokacin da Zamfara ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.”

Ya kuma caccaki gwamnan da cewa, a matsayinsa na wanda ya dace ya wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharsa, shi ke kokarin kawo rudu ga lamarin tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna na boye gaskiya, inji Shinkafi

Ya ce gwamnan na kokarin ririta lamari ne da boye gaskiya a lokacin da ya ce gwamnatin tarayya na tattaunawa da ‘yan bindiga.

Shinkafi ya bukace babban hafsan sojin kasar nan da ya samar da karin jami’an soji da kuma motocin yaki masu sulke na CSK saboda ragargazar ‘yan bindiga a maboyarsu.

Shinkafi jigo ne a fannin tsaro da ji da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a jihar Zamfara, kuma aikinsa ya yi tasiri ainun wajen tabbatar da tsaro a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dama-dama: Tinubu ya karawa ma'aikata albashi, amma akwai abin kura a gaba

An kwamushe dan bindiga a jihar Yobe

A wani labari na daban, jami’an ‘yan sanda sun kama shugaban wata tawagar masu garkuwa da mutane da neman kudin fansa a Damagum da ke Kolere da wasu sassan Tarmuwa da Dapchi a jihar Yobe.

An kama Mohammed Wada mai shekaru 35 dan kauyen Kanda ne a karamar hukumar Fune a unguwar Kolere da ke garin Fune, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan labari dai na fitowa ne daga rundunar 'yan sandan jihar, inda suka bayyana yadda aka kama tsageran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel