Siyasar Najeriya
Hadiman tsohon gwamnan jihar Ondo da ya gabata, Rotimi Akeredolu akalla uku sun aje aiki jim kaɗan bayan rantsar da Aiyedatiwa a matsayin sabon gwamnan jihar.
Fasto Osagie Ize-Iyamu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben 2024.
Wani babban malamin addinin islama, Sheikh Sulaiman Farooq Onikijapa, ya hango cewa nan gaba kaɗan Tinubu da Aregbesola zasu dawo inuwa ɗaya kamar da.
Rahotannin dake fitowa yanzu haka sun nuna cewa an yi nisa a bikin rantsar da Lucky Aiyedatiwa a matsayin sabon gwamnan jihar Ondo bayan mutuwar Akeredolu.
A yau Laraba ce aka rantsar da sabon gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar a kasar Jamus bayan ya sha fama da jinya.
Gwamnatin jihar Ondo ta sanar da rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu a hukumance ranar Laraba, ta kuma bayyana tsarin yadda za a masa jana'iza da binne shi.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya girgiza da mutuwar marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo inda ya bayyana shi a matsayin mutum marar tsoro ko kadan.
Dandazon mata sun fito sun yi dafifi domin cigaba da gudanar da zanga-zanga kan shari'ar zaben gwamnan jihar Adamawa. Sun bukaci ayi musu adalci.
Jam'iyyar All Progressives Congress, APC reshen jihar Kano, na zargin gwamnatin jihar ta NNPP da kokarin karkatar da kudaden kananan hukumomin jihar.
Siyasar Najeriya
Samu kari