Siyasar Najeriya
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Akpabio, ya yi zargin cewa duk wannan zanga-zangar da mutane ke yi kan tsadar rayuwa makirci ne da wasu suka shirya.
Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa Julius Abure, shugaban Labour Party na ƙasa ya shiga hannu ne bisa zargin yunƙurin kisa da mallakar makamai ba kan ƙaida ba.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun ƴan sanda sun kama Barista Julius Abure, shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na ƙasa a Benin City, babban birnin Edo.
Jagororin jam'iyyar PDP na shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya sun ayyana goyin bayansu ga Sunday Ideh-Okoye a matsayin wanda zai maye gurbin Anyanwu.
Hukumar yaƙi da marasa gaskiya EFCC na ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatahi Ahmed, kuma tuni tawagar lauyoyi suka isa Ilorin domin kai shi kotu.
Kungiyar NCRM ta taso shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a gaba sai ya yi murabus daga mukaminsa cikin gagawa. Ta jero dalilanta.
Wasu manyan ƙusoshi, Musa da Buba, sun haɗa kayansu sun fice daga babbar jam'iyyar adawa PDP, sun koma All Progressives Congress (APC) a shiyyar Kwara ta Arewa.
Babbar jam'iyar adawa ta ƙasa PDP ta rasa ɗaya daga cikin manyan ƙusoshinta a jihar Abia yayin da tsohon mataimakin kakakin majalisar dokoki ya sauya sheka zuwa APC.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Suleiman Kazaure, tsohon datakta janar na hukumar NYSC a matsayin shugaban kwamitin yaƙi da muggan ayyuka a makarantu.
Siyasar Najeriya
Samu kari