Bayan Tsige Gwamnoni 3, Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan APC a Arewa

Bayan Tsige Gwamnoni 3, Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan APC a Arewa

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta kori ƙarar jam'iyyar PDP ta ɗan takararta kan zaɓen gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia
  • Yayin yanke hukunci, kwamitin kotun ya tabbatar da nasarar Gwamna Rabaran Alia na APC a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris
  • Ta ce masu shigar da ƙara sun gaza gamsar da kotu kan ikirarin jabun takardu da suke zargin mataimakin gwamna, Samuel Ode

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da nasarar Gwamna Hyacinth Alia na jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Benuwai.

Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue.
Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Alia Na Jihar Benue Hoto: Hyacinth Alia
Asali: Facebook

Kotun ta ɗauki wannan mataki ne bayan ta kori ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna, Titus Uba, suka ɗaukaka zuwa gabanta, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan Kano, Mataimakin Shugaban APC ya faɗi kujerar gwamnan da zasu ƙwace a arewa

A ƙarar, PDP da ɗan takararta sun halubalanci hukuncin da ƙotun sauraron ƙorafe-korafen zaɓen gwamnan Benue ta yanke ranar 23 ga watan Satumba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko, ita kotun zaɓe ta kori karar da suka shigar suna kalubalantar nasarar Hyacinth Alia na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan zaben Benuwai

Kwamitin alƙalai uku na kotun ɗaukaka ƙara, a hukuncin da suka yanke iri ɗaya, sun warware dukkan ƙorafe-ƙorafen da masu ƙara suka gabatar.

Daga nan kuma kotun ta kori ƙarar gaba ɗaya saboda rashin cancanta kana ta tabbatar da hukuncin Kotun zaɓe, jaridar Vanguard ta ruwaito.

A cewar Kotun ɗaukaka ƙara korafe-korafen da masu ƙara suka gabatar batutuwa ne da suka shafi kafin zaɓe kuma sun gaza gamsar da kotu kan ikirarin da suka yi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Plateau ya bayyana matakin dauka na gaba bayan kotun daukaka kara ta tsige shi

Kotun ta ce PDP da ɗan takararta sun gaza gabatar da ƙwararan hujjojin da zasu tabbatar da zargin da suka yi cewa ɗan takarar mataimakin gwamna na APC, Samuel Ode, ya yi amfani da jabun takardu.

Abdullahi Abbas ya maida martani kan tsige Abba

A wani rahoton Shugaban APC ya sadaukar da nasarar da APC ta samu a Kotun ɗaukaka ƙara ga mutanen da rusau na Gwamnatin Abba ya shafa a Kano.

Abdullahi Abbas ya ce tsige Abba Gida-Gida a karo na biyu ya nuna cewa dama tun farko Gawuna ne ya ci zaɓen da aka yi a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel