Shari’ar Gwamnan Kano: Yan APC Sun Fara Azumin Neman Nasara Yayin da Abba Ya Garzaya Kotun Koli

Shari’ar Gwamnan Kano: Yan APC Sun Fara Azumin Neman Nasara Yayin da Abba Ya Garzaya Kotun Koli

  • Jam'iyyar APC ta bukaci mambobinta a jihar Kano da su dauki azumi tare da yin addu'o'in domin neman nasara a Kotun Koli kan shari'ar gwamnan jihar
  • Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya shigar da kara a Kotun Koli, inda ya kalubalanci hukun da Kotun Daukaka Kara ta yanke na tsige shi daga gwamna
  • Shugaban jam'iyyar APC na jihar ya ce akwai bukatar suma 'yan kasuwar da suka rasa dukiyoyinsu a rusau din da gwamnatin Kano ta yi, su yi azumi da addu'o'i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta yi kira ga daukacin mambobinta da duk ’yan kasuwar da suka yi asarar dukiyoyin a rusau din da gwamnati ta yi a jihar da su dauki azumi a yau.

Kara karanta wannan

Kano: Jigon NNPP ya tona asirin hanyar da APC ke bi don mayar da jihar karkashin ikonta saboda 2027

Shugaban jam’iyyar, Abdullahi Abbas, a cikin wani sakon murya da ya aike wa magoya bayan jam’iyyar, ya bukace su da su yi wa Allah godiya kan nasarar da jam’iyyar ta samu a kotun daukaka kara a ranar Juma’a.

Abba Kabir Yusuf
Saboda Gwamna Abba ya shigar da kara Kotun Koli, 'yan jam'iyyar APC sun shirya yin azumi don neman nasara Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamna Abba ya garzaya Kotun Koli

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakon nasa, kamar yadda Dailyt Trust ta ruwaito na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya yanke hukuncin kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara a Kotun Koli.

BBC Hausa ta ruwaito gwamnan na cewa ya umurci lauyoyin sa da su kalubalanci hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke, inda ya kara da cewa yana da kwarin gwiwar cewa “Kotun Koli za ta yi mana adalci."

NNPP ta bayyana matsayarta kan hukuncin Kotun Daukaka Kara

Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta bayyana bakin cikinta game da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, da ta kori gwamnan Kano, Abba Yusuf, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shari'ar gwamnan Kano: Jami'an tsaro sun bankado wani shirin tayar da tarzoma, sun gargadi al'umma

Jam'iyyar ta ce za ta binciki duk wata hanya ta doka da za ta kwato mata hakkinta.

Jami'in bincike na jam’iyyar na kasa, Ladipo Johnson, ya shaidawa jaridar The Nation cewa jam’iyyar za ta tunkari kotun koli da imanin cewa za ta samu nasarar kwato hakkinta da aka kwace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel