Ya Kamata a Tsame Hannun Alkalai a Harkar Zaben Najeriya, Falana Ya Fadi Dalilai

Ya Kamata a Tsame Hannun Alkalai a Harkar Zaben Najeriya, Falana Ya Fadi Dalilai

  • Babban lauya a Najeriya, Femi Falana ya bukaci Najeriya ta tsame hannun alkalai daga harkokin zabe na kasar
  • Falana, ya ce Najeriya ce kasa daya tilo a duniya da a yau alkalai ke yanke hukunci na karshe kan sakamakon zabe, don haka akwai bukatar a daina yin hakan
  • Lauyan ya yi nuni da cewa al’ummar Najeriya ne ya kamata su tantance wadanda za su mulke su ba wai alkalai 'yan kalilan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wani Babban Lauyan Najeriya (SAN), Femi Falana, ya ce ya kamata a tsame hannun alkalai a zaben Najeriya gaba daya.

Falana, wanda ya yi magana a cikin shirin Siyasa na ranar Lahadi, a gidan talabijin na Channels TV, ya ce ya kamata al’ummar Najeriya su tantance wadanda za su mulke su ba wai alkalai 'yan kalilan ba.

Kara karanta wannan

"Siyasar ubangida": Bidiyon Ododo duke a gaban Yahaya Bello ya haddasa cece-kuce

Femi Falana SAN
Falana ya ce ya kamata al’ummar Najeriya su tantance wadanda za su mulke su ba wai alkalai 'yan kalilan ba Hoto: Femi Falana SAN
Asali: Facebook

Ya na magana ne kan hukunce-hukuncen da kotu ta yanke na korar wasu gwamnonin, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A Najeriya kadai alkalai ke yanke hukuncin zabe - Falana

Jaridar Vanguard ta ruwaito shi yana cewa a Najeriya ne kawai alkalai ke yanke hukunci kan sakamakon zabe, yana mai kira ga kasar da ta yi koyi da abin da ya faru kwanan nan yayin babban zaben kasashen Laberiya da Saliyo.

Falana ya ce:

“Ya kamata masu ruwa da tsaki su koma kan teburin garambawul domin a kawar da hannun alkalai a zabenmu gaba daya."
“Najeriya ce kasa daya tilo a duniya da a yau alkalai ke yanke hukunci na karshe kan sakamakon zabe.
"Mun shaida yadda ta faru a kasar Laberiya, kasar da Najeriya ta taimaka wa wajen maido da kwanciyar hankali a siyasance, sun yi zabe cikin nasara."

Kara karanta wannan

'Jarabawa ce, gwamna ya yi martani kan hukuncin kotun da ta rusa zabenshi, ya sha alwashi

Babu bukatar sa hannun alkalai a harkokin zaben Najeriya - Falana

Ya kara da cewa:

"Kwanan nan, mun ga yadda zabe ya yi nasara a Saliyo, wata kasa kuma da Najeriya ta taimaka wa wajen ganin an dawo da doka da oda."
"Don haka, idan wadannan kasashe za su iya shirya zabe, me ya sa muke neman alkalai su tantance sahihanci na sakamakon zaben mu, babu bukatar hakan?"

Falana ya kuma ce a sake duba hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke na korar Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano da Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato.

Ya kuma ce bai kamata kotu ta lalata dubban kuri’u ba saboda jami’an INEC sun kasa buga stamfi akan kuri'un zaben.

Falana ya bukaci a sake duba hukuncin tsige gwamnonin Kano da Plateau

Babban lauyan Najeriya (SAN), Femi Falana, ya buƙaci a sake duba hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel