Femi Falana Ya Bukaci a Sake Duba Hukuncin Tsige Gwamnonin Kano da Plateau, Ya Bayyana Dalilansa

Femi Falana Ya Bukaci a Sake Duba Hukuncin Tsige Gwamnonin Kano da Plateau, Ya Bayyana Dalilansa

  • Femi Falana ya yi magana kan hukuncin da kotu ta yanke na korar wasu gwamnonin jihohi da bayyana sabbin waɗanda suka yi nasara
  • A wata hira da manema labarai, lauyan ya yi sharhi kan korar Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau da Abba Yusuf na Jihar Kano
  • Falana ya kuma buƙaci ƴan siyasa da su riƙa bin umarnin kotu a kodayaushe domin gujewa faruwar haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Babban lauyan Najeriya (SAN), Femi Falana, ya buƙaci a sake duba hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau.

Falana ya dau zafi kan tsige gwamnonin Kano da Plateau
Femi Falana ya yi kira a sake duba hukuncin tsige Abba da Mutfwang Hoto: Femi Falana, @Kyusufabba, @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Falana ya ɗau zafi kan korar gwamnonin Plateau, Kano da aka yi

Kara karanta wannan

Gwamnan Plateau ya bayyana matakin dauka na gaba bayan kotun daukaka kara ta tsige shi

Falana ya bayyana cewa hukuncin kotun da ya soke zaɓen Mutfwang da Yusuf, ya kamata a sake duba shi saboda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta gaza wajen gudanar da zaben da ya dace a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ce bai kamata kotu ta ɓata dubunnan ƙuri’u ba saboda jami’an INEC ba su sanya hannu kan ƙuri'u ba.

Babban lauyan wanda ya yi magana a cikin shirin Sunday Politics na Channels Television, ya ce bai kamata kotuna su soke ƙuri’un ƴan Najeriya ba, saboda sakacin hukumar zaɓe.

Falana ya bayyana dalilin da ya sa ya kamata a sake duba hukuncin

A cewar Falana, ya kamata a kammala batun zaɓe kafin kaddamar da kowace gwamnati.

Da yake magana kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, Falana ya ce INEC ta gaza yin aikin da ya dace kafin zaɓe da kuma lokacin zaɓe.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana matakin dauka na gaba bayan kotun daukaka kara ta tsige shi

Ya kuma buƙaci ƴan siyasa da dole su koyi yin biyayya ga hukuncin kotu.

Don haka ya bukaci duk wanda bai gamsu da hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar ba da ya garzaya kotun ƙoli.

A kalamansa:

"Idan ka duba abin da ya faru a Legas ya bambanta da abin da ya faru a Plateau. A Plateau akwai hukuncin da babbar kotu ta yanke na cewa sai an gudanar da zaɓen fidda gwani. Hukuncin, kamar yadda aka saba, an wulaƙanta shi kuma aka bijire masa sannan aka gudanar da zaɓe."
"Ya bambanta da Kano inda ake gaya mana cewa za a iya hukunta masu kaɗa ƙuri'a. Wannan wani tsarin shari'a ne mai hatsari a ce za a hukunta masu kaɗa ƙuri'a saboda kuskuren jami'an zaɓe."
"Ana ce mana ƙuri’u 165,000 sun lalace, ba su da inganci saboda wasu jami’an zaɓe sun yi kuskure ta hanyar ƙin buga musu tambari. Ta yaya hakan ya shafi ingancin zaɓe?

Kara karanta wannan

"Alhakin rusau ne" Shugaban jam'iyya na Kano ya maida martani mai ɗumi kan tsige Abba Gida-Gida

“Ina fata a wannan karon kotun ƙoli za ta warware waɗannan rigingimun da ba su dace ba a kan rashin sanya hannu a kan ƙuri'un zaɓe da jami'an INEC ke yi, wanda ba a bayar da shawarar a hukunta su ba."

Gwamna Mutfwang Ya Garzaya Kotun Ƙoli

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya umurci lauyoyinsa da su shigar da ƙara a kotun ƙoli kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige shi.

Gwamnan ya bayyana hukuncin a matsayin wani koma baya na wucin gadi, inda ya nuna ƙwarin gwiwarsa cewa zai samu adalci a kotun ƙolin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel