"Ba Na Kewar Kujerar Shugabancin Najeriya", In Ji Buhari

"Ba Na Kewar Kujerar Shugabancin Najeriya", In Ji Buhari

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce ba ya kewar lokacin da ya ke shugabancin Najeriya
  • A cikin wani gajeren sashi na hira da aka yi da shi, da aka saki a Twitter, ya nuna amsar Buhari kan tambayar da aka masa na abin da ya ke kewa bayan barin ofis
  • Buhari ya kuma yi magana kan lafiyarsa, yana mai cewa likitansa ne kadai zai iya bada amsa ta gaskiya game da lafiyarsa lokacin da ya ke mulki

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Daura, Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce baya kewar kasancewarsa shugaban kasar Najeriya.

Buhari ya yi magana ne yayin wata tattaunawa da ya yi da Gidan Talabijin na Najeriya (NTA).

Kara karanta wannan

Ka Canza Hali: Tsohon Shugaba a APC Ya Fadi Kuskuren Tinubu Daga Shiga Aso Rock

Buhari ya ce bai yi kewar lokacin da ya ke ofis ba
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi hira ta musamman da gidan talabijin na NTA. Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

A wani dan gajeren hira da aka wallafa a shafin X a ranar Lahadi, an tambayi tsohon shugaban ko ya yi kewar lokacin da ya ke ofis, ya bada amsa da cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kewa. Bana tunanin na yi kewarsa sosai."

A baya, Buhari ya ce ba zai yi kewar lokacinsa a ofis domin ana 'musguna masa'.

A watan Disamban 2022, tsohon shugaban kasa ya ce yana iya kokarinsa amma yan Najeriya ba su gamsu ba.

Amsar Buhari kan lafiyarsa

Legit Hausa ta lura cewa tsohon shugaban kasar ya shafe lokaci mai dan tsawo a mulkinsa wurin fita kasashen waje neman magani a Birtaniya.

Da aka masa tambaya kan irin rashin lafiyan da ke damunsa, Buhari ya ce:

"Ina tunanin likita na ne kadai zai iya bada amsa na gaskiya kan wannan tambayar."

A cewar NTA, za a saki cikakken hirar a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba misalin karfe 10 na dare.

Kara karanta wannan

Dan caca da ya ciyo N102m zai taimakawa dalibin da yayi asarar kudin karatunsa a caca

Yan Najeriya sun yi martani kan abin da Buhari ya fada

AMADA, @ahmad_muhalli_, ya ce:

"Ji yadda fatarsa ke sheki kuma hankalinsa kwance. Wannan shaida ne cewa ba ya kewar shugabancin kasa."

Sarkin Yaki na Buhari, @suleiman_qasim, ya ce:

"Mai gaskiya, ko ka zage shi, ko ka yabe shi, ka kira shi wanda ya gaza, ko ka kira shi rago amma ba za ka iya kiransa mai laifi ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel