NHIA: Ana Cikin Tsadar Rayuwa, Shugaba Tinubu Ya Yi Muhimmin Naɗi a Gwamnati

NHIA: Ana Cikin Tsadar Rayuwa, Shugaba Tinubu Ya Yi Muhimmin Naɗi a Gwamnati

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi sabon naɗi yayin da ƴan Najeriya ke kuka kan taadar rayuwa da wahalar da aka shiga a faɗin kasar
  • Shugaban ƙasar ya nemi majalisar dattawa ta tantance tare da tabbatar da naɗin Dakta Kelechi Ohiri a matsayin darakta janar na hukumar NHIA
  • Sanata Godswill Akpabio ya karanta sakon shugaba Tinubu kana ya miƙa lamarin ga kwamitin kiwon lafiya na majalisar dattawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci majalisar dattawan Najeriya ta amince da naɗin sabon shugaban hukumar inshoran lafiya (NHIA).

Tinubu ya naɗa Dakta Kelechi Ohiri a matsayin sabon shugaban hukumar NHIA kuma ya nemi sanatoci su tantance shi tare da tabbatar da naɗin, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya aike da buƙata 1 ga majalisar dattawa kan mutanen da ya naɗa a NAHCON

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Tinubu Ya Nemi Majalisar Dattawa Ta Amince d Naɗin Shugaban Hukumar NHIA Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Hakan na kunshe a wata wasiƙa da shugaban ƙasar ya aika ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, kuma ya karanta a zaman yau Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasiƙar mai taken, "Neman tabbatar da naɗin darakta janar na hukumar inshorar lafiya (NHIA)," ta ce:

“A bisa tanadin sashe na 40, karamin sashe na daya na dokar hukumar inshorar lafiya ta kasa ta 2022. Ina mai gabatar wa majalisa naɗin Dakta Kelechi Ohiri a matsyain darakta janar na NHIA domin tabbatar da shi."
"Ina fatan majalisa zata duba wannan buƙata kuma ta amince da naɗin."

Daga nan Akpabio ya mika bukatar ga kwamitin majalisar dattijai kan kiwon lafiya domin gudanar da aiki na gaba da kuma gabatar da rahoto a zauren majalisa cikin mako guda.

Shugaban ƙasa ya naɗa daractocin CBN

Wannan na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan shugaba Tinubu ya naɗa sabbin daraktoci 5 a babban bankin Najeriya (CBN).

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa mutum 5 a manyan muƙamai a babban banki CBN, ya tura saƙo Majalisa

A wata wasiƙa da ya aika majalisar dattawa, Bola Tinubu ya roƙi sanatocin su tantance tare da amince da naɗin daraktocin.

Nan take Sanata Akpabio ya miƙa sunayen ga kwamitin harkokin banki, kudi da hada-hadar kuɗi domin tantance mutanen tare da gabatar da rahoton cikin kwana 10.

Tinubu ya buƙaci tabbatar da shugaban NAHCON

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya aike da sako ga majalisar dattawan Najeriya kan naɗin shugaban hukumar jin daɗin alhazai da mambobi.

Shugaban ƙasar ya buƙaci sanatocin su tantance tare da amincewa da mutanen da ya naɗa bisa la'akari da kundin dokar NAHCON.

Asali: Legit.ng

Online view pixel