Yaron Sarki Ya Ci Zaben Majalisar Tarayya, Zai Zama ‘Dan Autan Majalisa a Shekara 32

Yaron Sarki Ya Ci Zaben Majalisar Tarayya, Zai Zama ‘Dan Autan Majalisa a Shekara 32

  • Sadiq Tafida Abbas yana shirin zama sabon ‘dan majalisar tarayya a sakamakon nasarar da ya samu wajen takara
  • Yaron Sarkin Muri mai shekara 32 ya yi galaba a kan sauran masu neman kujerar ‘dan majalisar Jalingo/Yoro/Zing
  • ‘Dan takaran na PDP zai gaji kujerar da Ismaila Maihanchi ya mutu ya bari ‘yan watanni kadan bayan an zabe shi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Taraba – Sadiq Tafida Abbas wanda mahaifinsa yake rike da sarautar kasar Muri ya yi nasara a zaben majalisar Jalingo/Yorro/Zing.

Farfesa Olarewaju Oladapo ya sanar da cewa jam’iyyar PDP tayi nasara a zaben cike gurbin da aka yi, Daily Trust ta kawo rahoton.

Sarki
Yaron Sarki zai je Majalisa Hoto: Sadiq Abbas Tafida/House of Representatives
Asali: Facebook

Sakamakon zaben da aka yi a Taraba

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya tona abin da ya jawo Wike ya goyi bayan Tinubu a kan Atiku a 2023

Sadiq Tafida Abbas ya samu kuri’u 19,681 wanda INEC ta tabbatar da sun fi na kowa yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Innocent Patrick (16,379) wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar SDP ya zo na biyu sai Aminu Malle (12,662) ya zo na uku a APC.

NNPP wanda ta shiga zaben a karkashin Aminu Abdu Liman ta samu kuri’u 3646.

Zababben 'dan majalisa zai tafi da kowa

Tafida Abbas ya mika godiya ta musamman ga Mai girma gwamna Agbu Kefas bayan nasarar da ya samu a zaben majalisar tarayyan.

Yariman ya yi alkawarin hada-kai da sauran abokan takararsa da kuma gwamnati mai-ci domin ya kawowa mazabarsa cigaba a Taraba.

An rahoto zababben ‘dan majalisar ya ce ya ziyarci wadanda ya gwabza da su daga sauran jam’iyyu, kuma duk sun yarda za suyi aiki tare.

Kara karanta wannan

NNPP ta yadu zuwa wajen Kano, Jam’iyya Ta Samu ‘Dan Majalisa a Jihar Nasarawa

Za a ci canji Hon. Ismaila Maihanchi a majalisa

Basaraken ya doke ‘yan takara goma wajen samun wannan nasara a PDP.

Leadership ta ce idan an rantsar da Tafida Abbas, zai zama wanda ya fi kowa karancin shekaru a zauren majalisar wakilan tarayya.

Abbas ya samu wannan kujera ne a sakamakon rasuwar Ismail Maihanci da aka zaba a 2023 ya wakilci mutanen Jalingo/Yoro/Zing.

Taron Sarakunan Arewa a Kaduna

Sarkin Musulmi da sauran Sarakunan Arewa sun yi zama a Kaduna, sun fadawa kan su da kuma gwamnati gaskiyar halin da ake ciki.

An rahoto Mai alfarma Sultan ya ce mutane suna cikin yunwa, amma har yanzu sun yi imani akwai masu fada masu kuma su saurara.

Sultan ya ce an shiga uku idan talaka ya daina jin maganar sarakuna da malamai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel