Hankalin Ganduje Ya Fara Kwanciya Bayan Samun Gagarumin Alkawari Daga Dattawan Jam’iyyar

Hankalin Ganduje Ya Fara Kwanciya Bayan Samun Gagarumin Alkawari Daga Dattawan Jam’iyyar

  • Yayin da Ganduje ke fuskantar barazana daga Arewa ta Tsakiya kan kujerarsa, akwai alamun zai samu natsuwa
  • Kungiyar dattawan jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiyan Najeriya ta goyi bayan Abdullahi Umar Ganduje
  • Wannan na zuwa ne bayan Sanata Ebute Ameh ya jagoranci tawagar zuwa sakatariyar jam’iyyar don nuna goyon baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Kungiyar dattawan jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiyan Najeriya ta goyi bayan Abdullahi Umar Ganduje.

Kungiyar mai suna North Central Stakeholders Forum ta nuna goyon baya da amincewa dari bisa dari da shugabancin Ganduje.

Dattawan APC sun marawa Ganduje baya yayin da yake fuskantar barazana
Dattawan APC a Arewa sun goyi bayan Ganduje. Hoto: Dakta Abdullahi Ganduje.
Asali: Original

Mene sakon dattawan APC ga Ganduje?

Ta bukaci Ganduje ya ci gaba da jagorancin jam’iyyar har bayan zaben 2027 don tabbatar da nasarar ta a zabe, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jam’iyyar PDP ta gaji da adawa marar amfani, za ta taimaki APC kan matsalar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ebute Ameh shi ya jagoranci tawagar zuwa sakatariyar jam’iyyar don nuna goyon baya.

Sun yabawa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar kan nuna rashin son kai da ya shafi addini da kabilanci da kuma yanki, Tribune ta tattaro.

Ebute ya nuna jin dadinsa kan yadda Ganduje ke gudanar da mulkin jam’iyyar musamman wurin amfani da sabbin tsare-tsare na fasaha.

Nasarorin da APC ta samu bayan hawan Ganduje

Ebute ya ce:

“Yayin da muka yi duba a dukkan bangarori, mun yanke hukuncin marawa Ganduje baya saboda ya taba ko ina da ake bukata a matsayin shugaba.
“Duk da akwai wadanda suke neman sauya shugabancin zuwa Arewa ta Tsakiya, amma shugaban jam’iyyar ya yi kokari matuka a kankanin lokaci.
“Har ila yau, jam’iyyar ta samu nasarori a zabuka da dama da aka gudanar tun bayan hawansa kujerar shugabancinta.”

Kara karanta wannan

NNPP ta yadu zuwa wajen Kano, Jam’iyya Ta Samu ‘Dan Majalisa a Jihar Nasarawa

Wannan na zuwa ne bayan rade-radin tumbuke Ganduje a kujerar don bai wa dan yankin Arewa ta Tsakiya.

Ganduje ya rasa jiga-jigan APC a Kano

Kun ji cewa jam’iyyar APC ta tafka asara bayan jiga-jigan jam’iyyar sun watsar da ita a Kano.

Wasu ciyamomin kananan hukumomi uku ne suka watsar da jam’iyyar tare da komawa jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar.

Ciyamomin sun hada da na Dawakin Tofa da Nassarawa da kuma Garum-Malam duk a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel