Daga Tono Badaƙalar N3.5bn, Mai Ajiyar Kuɗin Jam'iyyar Adawa Ta Ƙasa Ta Shiga Babbar Matsala

Daga Tono Badaƙalar N3.5bn, Mai Ajiyar Kuɗin Jam'iyyar Adawa Ta Ƙasa Ta Shiga Babbar Matsala

  • Rigimar cikin gida a jam'iyyar LP ta ɗauki sabon sabo yayin da fitacciyar jam'iyyar adawan ta ɗauki tsattsauran mataki kan babbar jigo
  • LP ta sauke ma'jiyi ta ƙasa daga kan muƙaminta kan rikicin da ya shiga tsakaninta da shugaban jam'iyya na ƙasa, Julius Abure
  • Hakan ya faru ne saboda Oluchi Opara ta zargi Abure da yin rub da ciki da kuɗin jam'iyyar kana ta nemi ya yi bayani kan kuɗin da aka tara na siyar da fom a zaɓen 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT Abuja - Kwamitin ayyuka (NWC) na jam'iyyar Labour Party ta ƙasa ya dakatar da mai ajiyar kuɗin jam'iyyar ta ƙasa, Oluchi Opara, na tsawon watanni 6.

Kamar yadda jaridar Punch ta tattaro, matakin dakatar da babbar jigon zai fara aiki ne nan take bayan sanarwa a wani taron manema labarai a sakateriyar LP da ke Abuja.

Kara karanta wannan

"Ba a kyauta mana": Soja ya fusata kan kyautar da Tinubu ya yi wa 'yan wasan Suoer Eagles

Labour Party.
Jam'iyyar Labour Party da Ma'ajiyinta Na Kasa Na Tsawon Watanni 6 Hoto: Julius Abure, Labour Party
Asali: Facebook

Meyasa LP ta dakatar da ma'ajiyi?

Idan baku manta ba a ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu, Opara ta kalubalanci shugaban LP na ƙasa, Julius Abure, da yin sama da faɗi da maƙudan kuɗin jam'iyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta buƙaci ya fito ya yi bayanin yadda aka kashe N3.5bn waɗanda aka tara daga siyar da fam din nuna sha'awa da tsayawa takara yayin harkokin babban zaɓen 2023.

Da take hira da Airse TV a cikin shirin 'Good Mornin Show' ranar Talata, Opara ta kuma yi iƙirarin cewa NWC karkashin Abure na cin amanar LP ta hanyar haɗa kai da gwamnatin Edo ta PDP.

Yayin da yake mayar da martani kan waɗannan zarge-zarge ranar Laraba, kakakin LP na ƙasa, Obiora Ifoh ya ayyana Opara a matsayin wacce ƴan adawa ke amfani da ita.

Ya ce LP ta yanke hukuncin dakatar da ita ne bayan ta gaza amsa gayyatar da kwamitin ayyuka NWC ya aika mata domin warware saɓanin, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Wani Mummunan Ibtila'i Ya Faru a Hedkwatar APC Ta Ƙasa a Abuja

Mai magana da yawun LP ya ce:

"Kwamitin ladabtarwa ya bada shawara ta hannun NWC cewa ya kamata a dakatar da Mis Oluchi Opara daga matsayin mai ajiyar kuɗin LP na tsawon wata 6 mafi ƙaranci, matakin zai fara nan take."

Ma'ajin LP ta tono badaƙalar N3.5bn

Rahoto ya zo cewa Ma'ajin jam'iyyar Labour ta kasa, Misis Oluchi Oparah ta nemi shugaban jam'iyyar na kasa ya ba da ba'asin yadda ya kashe kudaden jam'iyyar.

Misis Oparah na zargin cewa Mista Julius Abure, ya karkatar da akalla naira biliyan 3.5 na kudin fom din takara da jam'iyyar ta samu a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262