BoT: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa da Tsohon Gwamnan Kaduna Sun Samu Manyan Muƙamai

BoT: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa da Tsohon Gwamnan Kaduna Sun Samu Manyan Muƙamai

  • Jam'iyyar PDP ta tabbatar da Sanata Adolphus Wabara a matsayin shugaban kwamitin amintattu (BoT) na ƙasa
  • A taron BoT karo na 76 da aka yi ranar Talata, an kuma naɗa tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Maƙarfi, a matsayin sakataren kwamitin
  • Bayan haka ke kuma kwamitin ya nuna tsantsar damuwarsa kan halin matsin tattalin arziki, faɗuwar darajar Naira da tabarɓarewar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - People’s Democratic Party (PDP) ta tabbatar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara, a matsayin cikakken shugaban kwamitin amintattu (BoT).

Bayan haka kuma jam'iyyar ta naɗa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Maƙarfi, a matsayin sakataren BoT na PDP ta ƙasa.

Jam'iyyar PDP ta naɗa shugaban BoT da sakatare.
BoT: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa da Tsohon Gwamna Sun Samu Manyan Muƙamai | Hoto: PDP
Asali: Facebook

Maƙarfi zai maye gurbin tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabir Turaki, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jam’iyyar PDP ta gaji da adawa marar amfani, za ta taimaki APC kan matsalar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana wadannan nade-naden ne a karshen taron BoT karo na 76 da aka yi sakatariyar PDP ta ƙasa da ke Wadata Plaza a Abuja ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu.

An nada Wabara a matsayin shugaban riko na BoT na PDP a 2022, bayan tafiyar tsohon shugaban BoT Walid Jibrin, wanda ya yi murabus daga mukaminsa.

BoT-PDP ya aike da saƙo ga Shugaba Tinubu

Bayan kammala taron ranar Talata, kwamitin amintattun PDP ya roƙi shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shawo kan matsalar tsaro da kuma faɗuwar darajar Naira.

Sanata Wabara ya ce kwamitin ya nuna matukar damuwarsa kan matsin tattalin arziki da aka shiga da tsadar kayan masarufi da kuma matsalar karancin abinci a kasar nan.

A ruwayar Channels tv, sanarwan da kwamitin ya fitar bayan kammala taron ta ce:

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa mutum 5 a manyan muƙamai a babban banki CBN, ya tura saƙo Majalisa

"BoT na PDP na matuƙar danuwa da halin matsin tattalin arzikin da aka shiga da tsadar kayan masarufi, da kuma ƙarancin abinci wanda ya samo asali daga gurɓatattun manufofin gwamnatin APC.
"Mun kuma ankara da yadda sha'anin tsaro ya ƙara tabarbarewa duba da yawaitar kashe-kashe, ƴan bindiga, garkuwa da mutane da sauran ta'addanci musamman a watanni 9 da suka wuce.
"Kwamitin ya kuma nuna damuwa kan faɗuwar darajar Naira wadda yanzu ta kai N1,500 kan kowace dala, da kuma tashin farashin fetur da ya kai N700 duk lita, duk da haka ga dogayen layuka a gidan mai.
"Muna kira ha shugaban ƙasa ya sani mutane ba zasu iya jure wannan yanayi ba, ya tashi tsaye ya magance waɗannan matsaloli cikin gaggawa."

PDP ta shirya nemo mafita kan tsadar rayuwa

A wani rahoton kuma da ake cikin mawuyacin hali a Najeriya, jam’iyyar PDP mai adawa a kasar ta yi martani tare da alkawarin samo mafita.

Jam’iyyar ta ce madadin kushe tsare-tsaren gwamnati za ta yi kokarin yin adawa mai amfani ta hanyar neman mafita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel