Siyasar Najeriya
Shugaban APC na jihar Edo, Jarret Tenebe tare da wasu manyan ƙusoshi sun kai wa mataimakin gwamnan Edo Philip Shaibu ziyara har gida a Benin ranar Jumu'a.
Tsohon na kusa da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party, Doyin Okupe, ya musanta zargin cewa ya ci amanar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan a zaɓen 2023.
Yayin da ake tunkarar zaɓen gwamna a jihar Ondo, jam'iyyar PDP ta gamu da babban komawa baya a lokacin da Ebenezer Alabi ya sanar da raba gari da ita.
Kwamared Philip Shaibu, wanda kotu ta mayar kan kujerar mataimakin gwamnan jihar Edo ya zargi Gwamna Godwin Obaseki na shirya yadda za a kashe shi.
Ga dukkan alamu rigimar siyasa a jihar Edo za ta dawo sabuwa yayin Philip Shaibu ya tsallake Gwamna Godwin Obaseki, ya naɗa ma kansa sababbin hadimai.
Mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamared Philip Shaibu ya bayyana cewa shi ɗan APC ne amma abin da ya riƙe shi a PDP shi ne bai sanar da barinta a hukumance ba.
Jami'iyyar APC ta yi martani ga gwamnonin PDP bayan sun caccaketa kan jawo wahalar rayuwa a Najeriya, Kakakin APC, Felix Morka ya ce PDP ce babbar matsala.
Wanda ya kafa NNPP, Dakta Boniface Animeobonam ya musanta cewa an samu baraka a cikin jam'iyyar, amma ya ce akwai matsala da su ke fuskanta inda ya zargi Kwankwaso.
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa tun farko bai so zama mai tsawstarwa a majalisar dattawa ba saboda ya riga ya rike shugaban masu rinjaye a majalisa ta 8.
Siyasar Najeriya
Samu kari